Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Nuhu Ribadu Mashawarcin Musamman kan Harkokin Tsaro.
Sauran waɗanda Tinubu ya naɗa kan muƙamai daban-daban sun haɗa da Dele Alake wanda shi kuma aka naɗa shi Mashawarcin Musamman kan Ayyukan Musamman, Sadarwa da Tsare-tsare.
Yayin da shi kuma Wale Edun, tsohon Kwamishina a Legas, aka naɗa shi Mashawarcin Musamman kan Tsare-tsaren Harkokin Kuɗaɗe.
Sanarwar da Jami’in Yaɗa Labarai na Fadar Shugaban Ƙasa, Abiodun Oladunjoye ya fitar a ranar Alhamis, ta na ɗauke da cewa Ya’u Darazo an naɗa shi Mashawarcin Musamman kan Harkokin Siyasa.
An naɗa Olu Verheijen Mashawarcin Musamman kan Inganta Makamashi da Wutar Lantarki.
Tinubu ya naɗa Zachaeus Adedenji Mashawarcin Musamman kan Kuɗaɗen Shiga.
Yayin da John Ugochukwu aka naɗa Mashawarcin Musamman kan Masana’antu, Cinikayya da Zuba Jari.
Ita kuwa Salma Ibrahim an naɗa ta Mashawarcjyar Musamman kan Harkokin Lafiya.
Discussion about this post