Mambobin Majalisar Dokokin Jigawa ta zaɓi Haruna Aliyu matsayin sabon Kakakin Majalisar Dokoki.
Aliyu ɗan jam’iyyar APC ne, yayin da Sani Isyaku daga Gumel aka zaɓa Mataimakin Kakakin Majalisa.
An gudanar da zaɓen bayan da mamba daga Mazaɓar Malam Madori, Hamza Ibrahim ya nuna amincewar sa, tare da neman sauran su amince Aliyu ya zama Kakaki.
Nan da nan Mamba Muhammed Ibrahim daga Birnin Kudu ya amince da ƙudirin.
Daga sabon Kakakin har Mataimakin sa duk ba su samu abokan hamayya ba. Nan take Magatakardan Majalisa Musa Abubakar ya rantsar da su.
Kakakin Jigawa ya fito daga Ƙaramar Hukumar Miga, yankin Kudu maso Yamma na Jigawa. Gwamna Umar Namadi daga Arewa maso Gabas na Jigawa, shi kuma Mataimakin sa Aminu Usman daga Arewa maso Yamma.
Sai dai kuma ‘yan majalisar sun bijire wa wanda shugabannin APC na Jigawa su ka nemi ya zama kakakin majalisa, wato Idris Garba.
Bayan an rantsar da sabon Kakakin, nan da nan ya ɗage zaman majalisa zuwa ranar 23 Ga Yuni, ba tare da an zauna an ƙarasa zaɓen sauran shugabanni a majalisa ba.
An tabbatar da cewa kuma APC a Jigawa ta na da sunayen waɗanda ta ke so su zama shugaban masu rinjaye da kuma bulaliyar majalisa.
Shugaban APC na Jigawa, Aminu Sani bai halarci bukin rantsar da sabbin Kakakin Majalisa da Mataimakin sa ba.
PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda wasu magoya bayan APC daga Ƙaramar Hukumar Jahun su ka yi zanga-zanga a Majalisar Dokokin Jigawa, dangane da zaben Garba a matsayin sabon kakaki.
Sun nemi ba su yarda a sake zaɓen Garba a matsayin kakaki ba, domin shi ne ya sauka makonni biyu da su ka gabata, kuma ya yi kakaki tsawon shekaru bakwai.
Mambobi sun ƙi zaɓen Garba, sun zaɓi Aliyu, saboda mutanen sa daga Jabun ba su goyon bayan sake zaɓen Garba.
Akwai ‘yan majalisa 30, 29 na APC, 1 na PDP.
Discussion about this post