Duk da jan kunne da ake yi wa mata game da tafiya aikin Hajji alhali a na dauke da juna biyu, mata 75 ne aka samu suna ɗauke ciki bayan sun sauka kasa mai tsarki.
Hukumar Hajji ta kasa ta bayyana cewa akalla mata masu ciki 75 da aka gano suna ɗauke da ciki a kasa mai tsarki na kwance a asibitocin dake Makkah da Madina likitoci na duba su.
Wani likita daga cikin likitocin Najeriya Usman Galadima ya sanar da haka a lokacin da take zantawa da manema labarai a garin Makka ranar Laraba.
Galadima ya ce saboda yadda yanayin aikin hajji ya ke ya sa aka hana mata masu ciki zuwa da kuma zafin rana da ke wannan kasa, mace mara ciki ma yaya ta kare ballantana mai ciki.
Zuwa yanzu mata 45 na kwance a asibitoci a Makkah 30 na asibitoci a Madinah.
“Muna kira ga mata da su daina zuwa aikin haji idan sun san suna da ciki.
Bayan haka Galadinma ya ce hukumar na fama da mutanen dake fama da cututtukan da suka hada da hawan jini, ciwon siga da sauran su saboda da dama daga cikinsu ba su zo skin hajji da magungunan su ba.
Ya ce wasu da dama daga cikinsu mahukuntan Saudiyya sun kwace magungunan su tun a filin jirgin sama. Ya ce mahukuntan ba za su kwace magungunan ba idan an saka magungunan a cikin kwalayen su na ainihi.
Discussion about this post