Wani magidanci mai suna Mukhtar Ibrahim mai shekara 50 ya roki kotun shari’a dake Kaduna da ta fatattaki matarsa Sa’adatu Abdulhadi daga gidansa saboda ya gaji da auren.
Ibrahim ya fadi haka ne ta bakin lauyansa Jamilu Sulaiman inda yake cewa Ibrahim na bukatan kotun ta kara tabbatar wa Sa’adatu saki ukun da ya bata.
“Ina kuma rokon kotu ta bani izinin kula da ‘ya’yan mu hudu da muka haifa tare saboda bata da tarbiya na gari. Wata rana Sa’adatu ta kira ‘yan uwanta suka taru suka lakada mun dukan tsiya.
“Kulun hankali na a tashe yake saboda Sa’adatu ta ki barin gida na duk da saki ukun da na bata.
A ranar Laraba da kotun ta zauna Sa’adatu bata kotu duk da cewa an aika mata da sammace daga kotu.
Alkalin kotun Malam Isiyaku Abdulrahman ya dage shari’ar zuwa ranar 10 ga Yuli.
Lalacewar aure ya dade da zama ruwan dare a gidaje da dama.
Za a iya cewa rashin hakuri ne tsakanin ma’urata ko kuma ibtila’i ne ya fado a zamantakewar aure a gidaje da dama.
Abu kadan za ka ji ma’aurata sun je Kotu don kotu ta raba auren su koda iyaye sun shiga domin a sassanta su.
Abin takaicin shine yadda matsaloli irin haka bai tsaya ga sabbin aure ba, harda tsoffi da dama wadanda suka dade a cikin harkar ke fama da matsalolin.
Discussion about this post