Wani majalisa bada shaida a shari’ar zaɓen shugaban ƙasa, wanda Atiku da PDP su ka gabatar, ya shaida wa alƙalan kotun cewa INEC ta goge dukkan sakamakon zaɓen da ke cikin Na’urar Tantance Masu Shaidar Rajistar Katin Zaɓe, wato BVAS.
Wannan na’urar dai INEC ta saka su a dukkan rumfunan zaɓe sama da 176,000 a faɗin ƙasar nan, lokacin zaɓen 2023.
Mai bayar da shaida Hitler Nwala, wanda ƙwararren masanin sarrafa na’urorin zamani ne, ya shaida wa kotu cewa ya bibiyi BVAS 110 da aka yi zaɓe da su a FCT Abuja, amma ya samu duk INEC ta goge sakamakon zaɓen da ke cikin su, kafin hukumar zaɓen ta bayar a bibiye su.
Lauyan Atiku Abubakar, wato Chris Uche ne ya gabatar da mai bada shaidar.
A makon jiya kuma an gabatar da Dino Melaye a matsayin mai bada shaida, inda shi ma ya rantse a kotu cewa an yi ƙwange da aringizon sakamakon zaɓe don a kayar da Atiku.
Kakakin Yaɗa Labaran Kamfen ɗin Atiku Abubakar, Dino Melaye, ya bayyana gaban Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa, a matsayin mai bayar da shaida na Atiku Abubakar.
Melaye wanda ya bayyana a matsayin mai bayar da shaida na musamman ga Atiku Abubakar, ya bayyana cewa sakamakon ƙarshe na zaɓen shugaban ƙasa wanda INEC ta bayyana wa duniya, ba daidai-wa-daida INEC ɗin ta zuba su a kwanfuta ba.
Tsohon Sanata Dino shi ne mai shaida na 22 da Atiku ya gabatar a kotu.
Lauyan Atiku Chris Uche ne ya gabatar da Melaye, wanda ya shaida wa kotu cewa shi ne ejan ɗin PDP a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe.
Ya ce ya ƙi yarda ya sa hannu kan sakamakon zaɓen da INEC ta fitar, saboda ba a zuba su cikin kwanfuta kamar yadda ya dace ba.
Ya ce ya fice daga Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓen ce tun kafin a kai ga bayyana sakamakon zabe, bayan ya gano an yi burum-burum wajen zuba sakamakon zaɓe a kwamfuta don a kayar da Atiku.
Ya ce dalili kenan yawancin ejan na PDP a faɗin ƙasar nan ba su sanya hannu kan fam mai ɗauke da sakamakon zaɓe ba, wato mai lamba EC8As.
Discussion about this post