Ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin PDP, a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya bayyana aniyar gayyato ma’aikatan wucin-gadin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), domin su bayar da shaidar rashin sahihancin nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023.
Atiku ya ce zai gabatar da su ne a gaban Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa a Abuja.
Masu bayar da shaidar su uku, waɗanda za a gabatar a gaban alƙalan kotun, su na daga cikin ma’aikatan wucin-gadin zaɓen shugaban ƙasa, wanda INEC ta shirya a ranar 25 ga Fabrairu.
Atiku dai ya yi zargin an yi gagarimin maguɗi a faɗin ƙasar nan, ya shigar da ƙarar rashin amincewa da sakamakon zaɓen.
Ya nemi kotu ta ba shi nasara, ko kuma ta soke zaɓen a sake wani sabo daban.
Yayin da ake sauraren ƙarar da Atiku ya shigar a ranar Laraba, an kira mai bada shaida na 11 da Atiku ya gabatar.
Yayin da aka kira mai bada shaidar ɓangaren Atiku na uku, nan take sai waɗanda Atiku ya maka kotu wato Tinubu, APC da INEC su ka ce ba su yarda wanda Atiku ke so ya bayar da shaidar ya yi magana a gaban alƙalan.
Lauyoyin waɗanda Atiku ke ƙara ne, Abubakar Mahmoud na INEC, Akin Olujimi na Shugaba Tinubu da kuma Lateef Fagbemi na APC, duk sun yi tsuru-tsuru, sun kasa zaune, sun kasa tsaye, yayin da aka ce wanda zai bayar wa Atiku shaidar ma’aikacin wucin-gadi ne na INEC, kuma da shi aka shirya zaɓen 2023.
Lauyoyin sun riƙa magana ɗaya bayan ɗaya, su na shaida wa kotu cewa a ba su lokaci su yi nazarin bayanan da mai shaidar ya yi a rubuce.
Lauyan INEC ya ce ya na so a ba shi lokaci ya koma ya bi diddigin rekod ɗin aikin da mai shaidar ya yi a INEC, a baya.
A nan fa lauyan Atiku wato Chris Uche, ya shaida wa kotu cewa ai ma’aikacin INEC ɗin ba ma shi kaɗai ba ne zai bayar da shaidar, su uku ne, akwai sauran biyu kenan.
An yi ta ja-in-ja, har dai lauyan Atiku ya amince aka ɗage zaman zuwa washegari Alhamis domin bayar da shaida daga bakin ma’aikatan INEC.
Discussion about this post