Kotun majistare dake Kafanchan jihar Kaduna ta daure wani manomi mai shekaru 40, mai suna Zakaria Bulus a kurkuku bisa laifin yi wa ‘yar shekara 10 fyade.
Rundunar Sibul Difens NSCDC ta kama Bulus bisa laifin yi wa ‘yar shekara 10 fyade.
Alkalin kotun Samson Kwasu ya yi watsi da rokon sassauci da Bulus ya nema sannan ya yanke hukuncin daure shi a kurkuku har sai an kammala yin bincike a fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka.
Kwasu ya ce zai a ci gaba da shari’a ranar 18 ga Yuli.
Jami’in NSCDC Marcus Audu da ya shigar da karar a kotu ya ce mahaifiyar yarinyar ce ta kawo karar Bulus ofishin su ranar 13 Yuni.
Audu ya ce mahaifiyar yarinyar ta ce Bulus ya yi wa ‘yarta fyade bayan ya lallabeta zuwa wani kangon gini dake Ungwan Masara inda a nan ne ya danne ta.
Ya ce an samu tabbacin fyaden da Bulus ya yi daga sakamakon gwajin da aka yi wa yarinyar a asibitin Salama.
Sannan bayan ya shiga hannun jami’an tsaro Bulus ya tabbatar cewa shine ya yi yarinyar fyade.
Discussion about this post