Babban kotun tarayya da ke Kaduna ta umurci rundunar sojin Najeriya ta kyale mazauna garin Jaji dake nima a gonakin dake kusa da barikin sojoji su rika Noma.
Alkalin kotun Hannatu Balogun ta umarci rundunar ta biya mutum 260 dake zaune a Jaji suna noma a waɗannan gonaki Naira 1,000 sannan su gabatar wa kotu shaidar biyan kudin ranar 10 ga Yuli.
Lauyan da ya shigar da karar, Kimi Livingston ya kai karar babban kwamandan 1 Division da wasu manyan sojoji dake Jaji cewa sun ki yin biyayya ga umarnin kotu na dakatar da katange filayen mazaunan kauyukan dake kusa da barikin sojojin.
Livingston ya ce sojojin na hana wadannan monoma noma a filayen su da sojojin ke kokarin katangewa a cikin barikinsu.
A lokacin da kotu ta zauna babu sojan da ya zo kotu inda daga baya suka aiko wasikar cewa kwamandan 1 Division da sauran manyan ma’aikatan da ake kara an canja musu wurin aiki.
Alkalin kotun ta ki amincewa da haka
Lauyan dake kare sojojin Aliyu Ibrahim ya bayyana a kotun cewa zai tabbatar sojojin sun zo kotun a zama na gaba da za ta yi ranar 10 ga Yuli.
Ibrahim ya karyata hana mutane noma a ginakin su dake kusa da barikin sojoji cewa hakan bai faru ba.
Idan ba a manta ba a watan Nuwambar 2020 ne mazaunan kauyukan dake Jaji suka kai karar sojojin cewa sun hanasu noma a gonakin su da ke kusa da barikin sojojin.
Discussion about this post