Kotu dake Igboro a Ilorin jihar Kwara ta raba auren shekara 34 a dalilin rashin kauna tsakanin ma’auratan Ibrahim Aduke da Ishola Akanbi.
Alkalin kotun AbdulQadir Umar bayan ya raba auren ya bai wa Aduke ikon kula da ‘ya’yan su biyu mace mai shekara 14 da namiji mai shekara 6.
Alkalin ya ce Akanbi zai rika biyan Aduke naira 20,000 duk wata domin ciyar da ya’yan, zai Kuma biya kudin makarantar yaran da sauran bukatunsu sannan yana da ikon ganin su a duk lokacin da yake so.
A ranar 27 ga Maris Aduke ta shigar da kara kotu a raba auren ta da mijinta sannan kuma da neman kotun ta bata ikon kula da ‘ya’yan su.
Kotun ta dakatar da shari’ar saboda ma’auratan su sassanta amma hakan bai yiwuba.
A dalilin haka kotun ta raba auren saboda ma’auratan sun tabbatar cewa babu sauran kauna a tsakanin su.
Lalacewar aure ya dade da zama ruwan dare a gidaje da dama. Za a iya cewa rashin hakuri ne tsakanin ma’aurata ko kuma ibtila’i ne ya fado a zamantakewar aure a gidajen ma’aurata.
Abun da bai taka kara ya karya ba sai kaji ko miji ko mata za arce zuwa kotu, kawai a raba auren. Kuma abin tashin hankali a kai shine abin har da daɗaɗɗun aurarraki wadanda suka shekara har sama da 30.
Da ga rai ya baci shikenan sai kowa ya nemi kama gaban sa.
Discussion about this post