Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu jami’an Gwamnatin Jihar Katsina su biyu a kotu, bayan kama su da laifi karkata Naira Miliyan 289 zuwa aljifan su.
Waɗanda ake tuhumar su biyu wato Saadu Maiwada da Sani Lawal, sun tafka harƙallar ce a matsayin su na Babban Ma’aji da kuma Mataimakin Ma’aji a Ofishin Akanta Janar na Gwamnatin Jihar Katsina.
Sanarwar da ta fito daga Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ta ce an gurfanar da su ne a Babbar Kotun Jihar Katsina, bisa zargin su da aikata laifuka biyar da su ka shafi haɗa-baki su ka aikata cin amana da zamba.
An zarge su da laifin haɗa baki su ka karkatar da naira miliyan 289, mallakar gwamnatin Katsina, wadda su ka karkata cikin aljifan su, a cikin 2017.
“Bincike ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun karkatar da kuɗaɗen da su ka sata ta hanyar wani asusun ajiyar banki mai sunan Integrated Gas Services Limited, wanda kamfani ne da shi Sa’adu ke Darakta.
“Sun kuma kamfaci Naira miliyan 49, aka sake narkawa cikin asusun Integrated Gas Services Limited zuwa asusun Lawal BK, wanda shi ne Mataimakin Akanta Janar na jiha,” inji sanarwar.
Sun musanta aikata satar kuɗaɗen, kuma mai Shari’a ya bada belin su, bayan lauyar EFCC mai suna A’isha Tahar Habib ta roƙi kotu ta bayar da wata ranar ci gaba da sauraren shari’ar.
Lauyan waɗanda ake ƙara wato J B Isreal, ya nemi a ba shi beli da baki, amma lauyan EFCC ya ce tilas sai Israel ya nemi beli a rubuce tukunna.
Mai Shari’a Musa Ɗanladi ya ɗage sauraren ƙarar zuwa ranar 24 Ga Yuli.
Discussion about this post