NNPLC ya bayyana cewa ya cire hannun sa daga shigo da fetur Najeriya daga ƙasashen waje.
NNPCL ya yi wannan sanarwa ce ranar Alhamis, a shafin sa na Tiwita, cewa ta na hanzarta bayar da lasisi ga manyan ‘yan kasuwa domin su riƙa shigo da fetur daga waje.
A ranar Laraba ce dai Hukumar Ƙayyade Tsare-tsaren Fetur (NMDPRA), ta bayyana cewa daga watan Yuli mai kamawa ne ‘yan kasuwa za su riƙa shigo da fetur daga waje.
Shugaban Hukumar, Farouk Ahmed ne ya bayyana haka ga manema labarai, bayan kammala ganawa da manyan dillalan fetur.
Ya ce tunda an cire tallafin fetur, ya zama dole a buɗe ƙofa ga ‘yan kasuwa domin ba su damar shigo da fetur daga waje a sayar bisa ƙa’ida.
Saboda haka ya ce dalili kenan NNPCL zai rage yawan fetur ɗin da ya ke shigo da shi, domin miƙa ragamar ga ‘yan kasuwa, matsawar za su kiyaye ƙa’idojin da aka gindiya.
Ahmed ya ce yanzu NNPCL zai rage yawan wanda ya ke shigowa da shi zuwa kashi 30% ko ƙasa da kashi 40%, kamar yadda Dokar Fetur ta ce babu wanda zai ɗauki nauyin shigo da fetur fiye da kashi 40% shi kaɗai.
Kamfanin NNPCL ya ce yanzu ba shi kaɗai zai riƙa shigo da fetur a Najeriya ba.

Discussion about this post