Hukumar DSS, wato SSS, ta ce ta bankaɗo masu wani shirin haɗa zanga-zangar game gari, domin ɓata sunan Gwamnantin Tarayya.
Sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran SSS ya fitar ranar Asabar, ta na ɗauke da cewa wasu na shirya kamfen na ɓatanci, dangane da dakatar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele da kuma binciken sa da SSS ke yi.
Peter Afunanya ya ce gungun wasu ‘yan taya ɓera ɓari na shirin yin zanga-zanga a wurare daban-daban a Abuja da Legas, ɗauke da kwalaye su na muzanta Gwamnatin Tarayya da kuma SSS.
Afunanya ya ce masu shirya zanga-zangar za su nemi a saki Emefiele.
Daga nan ya yi gargaɗin cewa mutane su guji shiga sabgar da babu ruwan su, domin ba wanda zai iya hana SSS aikin su.
Cikin makon jiya, tsohon lauya ya ce EFCC da ICPC ne ya kamata su kama Emefiele, amma ba aikin SSS ba ne.
Kungiyar Lauyoyi
Tsohon Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA), ya bayyana abin da ya kira “damuwar sa”, dangane da kamun da Hukumar Tsaro ta SSS ta yi wa dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Agbakoba ya ce babu wani ƙorafi don an dakatar da Emefiele, amma dai shi bai ga dalilin da zai sa SSS su kama shi ba, tunda su dai babu ruwan su da shiga lamarin laifukan da su ka shafi harkokin tattalin arziki ko kuɗaɗe.
“Aikin SSS shi ne tabbatar da tsaron cikin gida, wato cikin ƙasa. To me zai kai su ga kama Emefiele?
“Abin mamakin shi ne yadda sauran hukumomin da ke da haƙƙin binciken harkokin zambar kuɗaɗe su ka yi shiru, har yau ba su ce komai ba dangane da Emefiele, tun bayan dakatar da shi. Sai kawai ji mu ka yi SSS sun ce ya na hannun su. In dai ba zargin aikata zagon ƙasa ga gwamnati ba, me zai kai SSS su kama shi?” Inji Agbakoba.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin kama Emefiele da SSS yi, sannan aka jefa shi magarƙama bayan Tinubu ya dakatar shi.
A cikin labarin kuma an bayyana yadda SSS su ka zarge shi da laifin taimaka wa ‘yan ta’adda da kuɗaɗe, amma kotu ta hana kama shi a cikin Disamba, saboda rashin ƙwaƙƙwarar hujja.
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) ta bayyana cewa ta kama dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele.
DSS sun kama shi, ba da daɗewa ba bayan Gwamnatin Tarayya ta bayar da sanarwar dakatar da shi.
Sanarwar da damƙe Emefiele ta fito daga bakin Kakakin Yaɗa Labaran SSS, Peter Afunanya, a cikin wata sanarwar manema labarai da ya raba, ya aiko wa PREMIUM TIMES.
“Lallai dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele na hannun mu. Ya na tsare ne aka yi masa wasu tambayoyi dangane da binciken da ake yi kan sa.” Haka dai Afunanya ya rattaba a ciki sanarwar da ya aiko wa PREMIUM TIMES.
Idan ba a manta ba, cikin watan Disamba, 2022 SSS sun nemi kama shi domin zargin ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda, amma kotu ta hana su, saboda rashin ƙwaƙƙwarar shaida.
Discussion about this post