Wata matar aure Maryam Musa ta kai karar mijinta Kabiru Sulaiman kotun shari’a dake Magajin Gari a Kaduna inda take rokon kotu ta hana mijinta jibgar ta kamar yadda ya saba.
Maryam ta ce saboda da rashin jituwar da suka samu a kwanakin baya Sulaiman ya rika lakada mata duka sannan ya kora ta zuwa gidan Iyayen ta.
“A wannan rana Sulaiman ya shake ni a wuya, ya naushe ni a ciki sannan ya watsar mini da kaya na a waje ya kulle kofa.
“Har yanzu ina son Sulaiman amma duka da cin zarafi na da yake yi na ya yi matukar yawa. Idan har ba zai Daina cin zarafina ba zan hakura kawai da auren.
Lauyan Sulaiman, Jamilu Sulaiman ya karyata duk abin da Maryam ta fadi a kansa.
Sulaiman ya ce shi ko da wasa bai taba daga hannu da sunan ya duki matarsa ba.
Ya roki kotun da ta basu lokaci su sassanta kansu domin shima yana son matarsa Maryam.
Alkalin kotun Malam Isiyaku Abdulrahman ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 20 ga Yuli.
Cin zarafin mace da maza ke yi na daga cikin matsalolin dake kashe aure a wannan zamani.
Wasu lokutan mazan basu da laifi, matan ne ke ingiza su suna cin zarafin su saboda rashin tarbiyya da taurin kai irin ta su.
Discussion about this post