Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa dimokuraɗiyya a Najeriya ta samu gindin zama ne a Najeriya yanzu saboda irin gudunmawar da mutane irin su MKO Abiola suka bada.
A jawabin ranar Dimokuraɗiyya wanda shugaba Tinubu ya yi ranar Litinin, ya ce ” Abiola ya sadaukar da rayuwar sa saboda dimokraɗiyya a kasar nan ya samu gindin zama Kuma akan haka ne yake har ya koma ga Allah.
Tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida ya soke zaɓen a daidai ana gab da bayyana marigayi Abiola
wanda ya yi nasara a zaɓen.
Wannan abu na Babangida ya yi ya kawo matsaloli da dama a siyasar Najeriya. Da yawa cikin waɗanda suka yi adawa da mulkin soji a wancan lokaci a kasar nan sun arce daga Najeriya saboda tsoron kada a kama su.
Zaben Abiola na daga cikin zaɓukan da aka yi a a kasar nsn da kowa yayi na’am da sahihancin sa, amma kuma sojoji suka soke zaɓen da karfin tsiya.
Tinubu ya ce gwamnatinsa ta al’umma ce kuma za ta fi maida hankali ne wajen tabbatar da ganin talaka ya amfana da arzikin kasar.
Yayi kira ga ƴan Najeriya da su ci gaba da yi wa kasa addu’a da kuma mara wa gwamnati baya domin samun nasara.
Discussion about this post