Shugaba Bola Tinubu ya roƙi ‘yan Najeriya cewa su ci gaba da juriya da sadaukarwar da su ke kan yi, ya ce nan gaba kaɗan za a ga haske daga matsin da ƙasar nan ke fuskanta.
Da ya ke jawabi a ranar 12 Ga Yuni, ranar da aka ware don tunawa da zaɓen 12 ga Yuni, 1993, Tinubu ya ce gwamnatin sa za ta yi wa ‘yan Najeriya sakayya da muhimman ayyukan raya ƙasa kamar bunƙasa harkokin sufuri, inganta ilmi, samar da wutar lantarki wadatacciya, inganta kiwon lafiya da sauran hanyoyin kyautata rayuwar jama’a.
Ya hori waɗanda ke kan muƙamai na mulki a matakai daban-daban cewa su ƙara cusa wa zukatan su kishin ƙasa da janjircewa wajen sadaukar da kai ga yin aiki tuƙuru.
A na sa ɓangaren, Tinubu ya ƙara jaddada cewa zai cika alƙawurran da ya ɗauka a lokacin kamfen, tare da yin mulki mai adalci.
Da ya koma kan zaɓen 12 ga Yuni, 1993, wanda marigayi MKO Abiola ya lashe, amma sojoji su ka dankwafar da dimokraɗiyya a lokacin, Tinubu ya ce ya kamata hakan ya zama wata allurar ƙara zaburar da shugabanni a yanzu su ƙara tashi tsaye sosai wajen kare dimokraɗiyya.
Tinubu ya jinjina wa Abiola, bisa tsayuwar sa wajen ganin ya kare dimokraɗiyya da gumin sa kuma da jinin sa.
Ya tunatar da ‘yan siyasa cewa, “duk wanda ba shi da nimirin shanye dafin kibiyar faɗuwa zaɓe, to wannan bai san muhimmancin shugabanci ba.”
Zaɓen ranar 12 Ga Yuni, 1993 dai shugaban mulkin soja na lokacin, Janar Babangida ne ya soke shi.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Babangida, wanda aka fi sani da laƙabin IBB, ya soki ‘yan siyasa, shekaru 30 bayan ya soke zaɓe sahihanci.
Tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida mai ritaya, ya hori ‘yan siyasa cewa su yi amfani da ribar zaɓen 12 ga Yuni, 1993 domin su ƙara wa daɓen dimokraɗiyya makuba.
Babangida ya yi wannan bayani a Minna, yayin ganawar sa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), tattaunawar da su ka yi a kan dimokraɗiyya.
“Ribar zaɓen ranar 12 ga Yuni, 1993, zaɓe na shugaban ƙasa, ina ganin har yanzu ‘yan siyasa ba su yi amfani da wannan ribar ba a zaɓukan da su ka biyo na 12 ga Yuni ɗin.
“An yi ittifaƙin cewa shi ne zaɓe mafi sahihanci da inganci a tarihin zaɓukan da aka yi a ƙasar nan. Amma kuma har yau ‘yan siyasa sun ƙi amfani da darussan da wannan sahihin zaɓe ya koyar.
“Ku tuna shi ne zaɓen da ‘yan Najeriya su ka yi tururuwar fita domin su zaɓi shugabannin su.”
Da Babangida ke magana ta bakin Kakakin Yaɗa Labaran Babangida, Kasim Afegbua, Babangida ya ce, “A yanzu dabanci da tashin hankula sun yi yawa.”
Babangida ya nuna rashin jin daɗin yadda a shekarun da su ka gabata zuwa yau, a lokacin kowane zaɓe za ka ga masu jefa ƙuri’a sai raguwa su ke yi a lokutan zaɓe.
“Kamata ya yi a ce zaɓen 12 Ga Yuni ya ƙara zaburar da jama’a tururuwar fita su jefa ƙuri’a dandazo-dandazo, ta yadda dimokraɗiyyar za ta ƙara karsashi a idanun jama’a. Amma abin takaici yawan masu jefa ƙuri’a sai raguwa su ke yi, maimakon a ce su na ƙaruwa sosai da sosai.”
Discussion about this post