Shugaba Bola Tinubu ya ja kunnen musamman ‘yan siyasa cewa su guji garzaya kotuna don biyan buƙatar kan su, su na karɓo umarni daga kotu da nufin gurgunta dimokraɗiyya.
“Saboda a fili abin ya ke cewa akwai masu garzayawa kotu su na karɓo umarnin da bai zama tilas ba, kuma ba bisa ƙa’ida ba, don kawai su kawo wa dimokraɗiyya cikas.
“Don haka ba za mu lamunci masu irin wannan baƙar aniya ba, sai dai aniyar su ta bi su.”
Da ya ke magana kan zaɓen 2023 wanda ya ba shi nasara, Tinubu ya yi jirwaye mai kama da wanka ga waɗanda ke shari’a da shi a kotu.
“Duk waɗanda ba su iya jure zafin faɗuwa zaɓe, to ba su cancanci jin daɗin samun nasara ba, idan nasara ta juyo kan su.”
Ya hori ‘yan Najeriya cewa su daure, su bi shi kada su sare, hanyar da zan bi da su mai ɓullewa ce.
Shugaba Bola Tinubu ya roƙi ‘yan Najeriya cewa su ci gaba da juriya da sadaukarwar da su ke kan yi, ya ce nan gaba kaɗan za a ga haske daga matsin da ƙasar nan ke fuskanta.
Da ya ke jawabi a ranar 12 Ga Yuni, ranar da aka ware don tunawa da zaɓen 12 ga Yuni, 1993, Tinubu ya ce gwamnatin sa za ta yi wa ‘yan Najeriya sakayya da muhimman ayyukan raya ƙasa kamar bunƙasa harkokin sufuri, inganta ilmi, samar da wutar lantarki wadatacciya, inganta kiwon lafiya da sauran hanyoyin kyautata rayuwar jama’a.
Ya hori waɗanda ke kan muƙamai na mulki a matakai daban-daban cewa su ƙara cusa wa zukatan su kishin ƙasa da janjircewa wajen sadaukar da kai ga yin aiki tuƙuru.
A na sa ɓangaren, Tinubu ya ƙara jaddada cewa zai cika alƙawurran da ya ɗauka a lokacin kamfen, tare da yin mulki mai adalci.
Da ya koma kan zaɓen 12 ga Yuni, 1993, wanda marigayi MKO Abiola ya lashe, amma sojoji su ka dankwafar da dimokraɗiyya a lokacin, Abiola ya ce ya kamata hakan ya zama wata allurar ƙara zaburar da shugabanni a yanzu su ƙara tashi tsaye sosai wajen kare dimokraɗiyya.
Tinubu ya jinjina wa Abiola, bisa tsayuwar sa wajen ganin ya kare dimokraɗiyya da gumin sa kuma da jinin sa.
Ya tunatar da ‘yan siyasa cewa, “duk wanda ba shi da nimirin shanye dafin kibiyar faɗuwa zaɓe, to wannan bai san muhimmancin shugabanci ba.”
Discussion about this post