Kodinatan rusasshiyar Rundunar Kamfen ɗin Tinubu (PCC) na Jihar Zamfara, tsohon Sanata Kabir Marafa, ya tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu zai cika alƙawarin da ya ɗauka cewa zai saka wa dukkan ‘yan jam’iyya waɗanda su ka taya APC kaiwa ga nasara da muƙaman da su ka dace da kowanen su.
Marafa ya yi wannan tabbacin a a ranar Talata, a lokacin da ya ke taron walimar cin abinci tare da mambobin rundunar na jihar Zamfara a Abuja.
Mambobin sun zo Abuja domin su halarci bikin rantsar da Tinubu, sai dai kuma wasun su ba ma samu katin gayyata shiga Dandalin Eagle Square, inda aka yi taron ba.
Bayan rantsar da shi dai yanzu kowa ya zura idanu ya ga sunayen mutanen da Tinubu zai ɗauka ministocin sa, sai kuma sauran muƙamai daban-daban.
Marafa, wanda tsohon sanata ne, ya bai wa tawagar mambobin rusasshiyar PCC haƙuri, saboda bayan sun niƙi gari daga Zamfara sun je Abuja taron rantsar da Tinubu, ba a bari sun shiga wurin taron ba.
“Lokacin da aka yi kura da shan bugu, gardi da kama kuɗi ya wuce”, ya ce Shugaba Tinubu zai saka wa dukkan waɗanda su ka yi wa APC ɗawainiya hear aka samu nasara.
Kada Ku Tausaya Min Don Na Faɗi Zaɓen Sanatan Zamfara:
Marafa, wanda ya faɗi zaɓen Sanatan Zamfara, ya ce ma mahalarta taron liyafar cewa kada su tausaya masa son Aliyu Iƙra Bilbis na PDP ya kayar da shi.
Bilbis ya samu ƙuri’u 102,86, shi kuma Marafa ya samu 91,216.
Bayan faɗuwar da Marafa ya yi a APC, a zaɓen gwamna ma APC ta faɗi a Zamfara, inda Dauda Lawal ya kayar da tsohon Gwamna da ke kan mulki a lokacin, Bello Matawalle.
“Ai abin tausayi shi ne wanda bai tashi ya taɓuka komai ba. Amma rashin nasara ai taki ce ga shuka. Ba koyaushe ake nasara ba. A nema ba a samu ba ma ai wata nasarar ce, domin za a koyi darasi.” Inji shi.
Discussion about this post