Shugaba Bola Tinubu ya sa wa dokar kafa Bankin Ɗalibai hannu. Wannan bankin dai zai riƙa bai wa ɗalibai bashin da babu kuɗin ruwa a cikin sa.
Hadimin Tinubu Dele Alake ne ya bayyana haka a ranar Litinin, inda ya shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa cewa Tinubu ya sanya wa dokar hannu.
Idan ba a manta ba, a cikin ‘Ƙudororin APC’, wanda Buhari ya yi kamfen da su a 2015, an rattaba cewa a farkon mulkin Buhari za a riƙa bai wa ɗalibai lamunin kuɗaɗe ba tare da an caje su kuɗin ruwa ba.
“Gwamnatin Tarayya ce za ta riƙa biya wa ɗaliban kuɗaɗen ruwan da za su biya bankin.” Haka dai Ƙudirorin da Buhari ya yi kamfen da su ya bayyana a farkon shafin daftarin.
Sai dai shi wannan ƙudiri wanda Tinubu ya sa wa hannu, tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ne ya bijiro da shi tun cikin 2016.
A yanzu Gbajabiamila shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, yayin da ya fara aiki a ranar Laraba.
Wannan doka, “za ta sauƙaƙa samun damar karatu ga ‘yan Najeriya a manyan makarantun gaba da sakandare.”
Dama a kamfen ɗin TInubu ya yi alƙawarin ganin da zarar ya zama shugaban ƙasa, to zai sanya wa ƙudirin hannu domin ya zama doka, domin inganta harkokin ilmi a Najeriya.
Kasafin 2023 da Buhari ya yi dai an ware wa ɓangaren ilmi Naira tiriliyan 1.0, wato kashi 5.3% na ilahirin kasafin 2023 kenan. Kasafin na ilmi ya yi kaɗan sosai, domin Hukumar Ilmi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), ta ƙayyade cewa “ƙasashe masu tasowa su riƙa kashe aƙalla kashi 15% na Kasafin Kuɗaɗen su a fannin ilimi.
Discussion about this post