Hukumar ICPC ta sake maka tsohon Shugaban JAMB da NECO kotu, wannan karon har ma da ‘ya’yan sa huɗu, bisa wata sabuwar tuhumar satar maƙudan kuɗaɗe da azurta kan sa da iyalan sa.
An gabatar da Dibu Ojerinde a ranar Alhamis, a Babbar Kotun Tarayya Abuja, tare da ‘ya’yan sa Mary, Olumide, Adebayo da Oluwaseun.
Akwai kuma kamfanoni shida da aka maka kotun, waɗanda duk an gano mallakar Farfesa Ojerinde ne.
Fayil ɗin shari’ar shi ne mai lamba FHC/ABJ/119/2023.
ICPC ta gurfanar da su a gaban Mai Shari’a Obiora Egwuatu, tun cikin Yuli, 2021 bisa tuhuma 18 a wancan lokacin baya.
PREMIUM TIMES ta buga labarin tuhumar da ake yi masa a Babbar Kotun Minna, Jihar Neja.
Dama kuma akwai wasu kadarorin sa da kotu ta umarci ICPC ta ƙwace kafin kammala shar’a.
Tuhumar Da Ake Wa Ojerinde A Babbar Kotun Minna:
Yadda Tsohon Shugaban Hukumar Jarabawar NECO Da JAMB Ya Kwashe Kuɗaɗen Ɗalibai, Ya Gina Kamfanoni, Gidajen Haya, Gidajen Mai Da Danƙara-danƙaran Makarantun ‘Ya’yan Masu Hali:
Cikin Fabrairu, 2022, wannan jairda ta buga labarin kallo ya koma Babbar Kotun Minna da ke Jihar Neja, inda a ranar Alhamis mai shaida, kuma gogarman taya ɓarawo jidar kuɗaɗe, ya fallasa yadda tsohon Shugaban Hukumar Shirya NECO da JAMB ya mallaki wasu kadarorin Naira miliyan 341.9.
Mai bayar da shaidar mai suna Jimoh Olafunde, ya ce Dibu Ojerinde ya kwashi kuɗaɗen ya kashe su wajen gina kamfanin buga takardu, danƙareriyar makarantar ‘ya’yan masu hali da sauran kadarorin maƙudan kuɗaɗe.
Ojerinde ya yi Shugaban NECO tsakanin 1999 zuwa 2012. Sannan ya yi Shugaban JAMB daga 2012 zuwa 2016.
Bayan saukar sa ne aka naɗa Farfesa Ishaq Oloyede, wanda a shekarar farkon naɗa shi ya tara Naira Biliyan 5. Kafin nan kuwa a zamanin Ojerinde JAMB ba ta taɓa tara sama da Naira miliyan 300 ba.
Mai bayar da shaidar wanda Mataimakin Darakta ne kuma Shugaban Baitilmalin NECO, ya shaida wa kotu cewa, “Mu dai mun riƙa bin duk wata ƙa’ida wajen bayar da kwangiloli. To amma fa mun san abin da ya riƙa faruwa ta ƙarƙashin ƙasa wanda lamari ne da ya fi ƙarfin mu.
“Bari na bada misali, tsakanin 2904/2005, yawancin takardun da aka riƙa bugawa duk an riƙa bayar da kwangilolin ga wasu kamfanoni 17 mallakar wani abokin Farfesa Dibu Ojerinde. Shi ne aka riƙa bai wa duk wata kwangilar buga takardun jarabawar NECO.”
Mai gabatar da shaida ya riƙa bayyana yadda aka riƙa gabzar kuɗaɗe ana biyan kamfanonin da ya ce na bogi ne domin Ojerinde ya kafa kamfanin buga takardu.
An kuma gabatar da kwafe-kwafen takardun shaida ko hujja.
Wannan shari’a daban ta ke da wadda ake yi wa Ojerinde, ta zargin satar Naira biliyan 5.2 a Babbar Kotun Tarayya, Abuja.
Satar Naira Biliyan 5:2: Yadda Mai Bada Shaida Ya Fallasa Yawan Kamfanoni Da Maka-makan Gine-ginen Da Tsohon Shugaban Hukumar NECO Da JAMB Ya Mallaka:
A ci gaba da shari’ar tsohon Shugaban Hukumar NECO da JAMB, Dibu Ojerinde da ake yi, wani mai bada shaida wanda Hukumar ICPC ta gabatar a kotu, ya shaida wa Mai Shari’a yadda Ojerinde ya mallaki manyan kamfanoni da maka-makan gidaje, daga cikin naira biliyan ɗin da ake tuhumar su salwanta a hannun sa.
Wannan mai bayar da shaida na farko dai ya fara bayar da shaidar sa, yayin da ƙoƙarin daidaitawa ta hanyar ‘plea bargain’ ba ta yiwu ba.
‘Plea bargain’ shi ne ɓarawon gwamnati ya amince ya saci kuɗin, kuma zai mayar da su. Saboda haka kotu za ta yi masa sassaucin hukunci.
An dai yi ƙoƙarin wannan tattauna batun ‘plea bargain’ a ranar Laraba.
Mai Gabatar da ƙara ya shaida wa Mai Shari’a a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja cewa tsohon Rajistaran JAMB ya mallaki manyan kantama-kantaman kadarori na maka-makan gidaje da kanfanoni a lokacin da ya ke Rajistara na JAMB.
Peter Oyewole, wanda garin su ɗaya da Ojerinde, ya shaida wa kotu cewa ya yi aiki ƙarƙashin Ojerinde a matsayin lauyan sa. Ya ci gaba da bayar da shaida kan abin da ya san Ojerinde ya saya da naira biliyan 5.2 ɗin da ake tuhumar sa da sacewa.
Tun a cikin watan Yuli 2021 ne ICPC ta gurfanar da shi kotu, inda ake tuhumar sa da laifuka 18 da suka ƙunshi satar naira biliyan 5.2
ICPC ta ce ya saci kuɗin tun daga lokacin da ya ke Rajistara na NECO har zuwa lokacin da ya ke Shugaban JAMB.
Idan ba a manta ba, cikin watan Afrilu 2020, PREMIUM TIMES Hausa ta buga cewa ICPC ta ƙwace kadarorin biliyoyin nairori daga hannun Ojerinde, waɗanda suka haɗa da makarantu masu zaman kan su, gidajen mai, gidaje a jihohin Kwara da Oyo, waɗanda ya mallaka ta hannun ‘yan-kore a Ilorin, Ibadan da Ogbomoso.
Akwai kuma wasu a Ile Ife a Jihar Osun da kuma Abuja.
A ranar Talata Ojerinde ya nemi Kotu ta ɗage Shari’a zuwa kwana ɗaya, domin a ba shi damar ƙulla yarjejeniyar ‘plea bargain’.
Sai dai kuma an ci gaba da shari’ar a ranar Laraba, yayin da lauyan ICPC Ebenezer Shogunle ya sanar wa kotu cewa yarjejeniyar ba ta yiwu ba.
Daga nan ne Oyewole ya ci gaba da shaida wa kotu yadda shi da Ojerinde suka riƙa kafa kamfanoni da kuma sayen manyan kadarori na shi Ojerinde ɗin, a lokacin ya na Rajistaran NECO da kuma Shugaban JAMB, shi kuma Oyewole ya na lauyan sa.
Ya ce baya ga kamfanoni takwas da manyan gidaje da gidajen mai, har tulin hannayen jari Ojerinde ya saya a bankuna.
Za a ci gaba da shari’ar a ranakun 4 da 5 Ga Afrilu, bayan an damƙa wa kotu kwafe-kwafen takardun shaidu na rasiɗai da satifiket na shaidun mallakar kadarori a lokacin gabatar da shaidar.
Discussion about this post