Gaskiya ne da Hausawa ke cewa ‘noma babbar sana’a’, wani mawaƙi kuma sai ya ƙara da cewa ‘kowar yi ka, ya bar rasawa’.
Wannan karin magana ta yi matuƙar tasiri idan aka dubi irin gagarimin ci gaban harkokin bunƙasa dabarun noma na zamani da Hukumar Bunƙasa Noma da Kiwo ta ƙirƙiro sannan kuma ta tabbatar da tabbatar da shirin ya kai gaci.
Shirin ya samu gagarimar nasara ce, biyo bayan yadda Gwamnatin Jihar Kano ta haɗa kai da Bankin Musulunci, tare da sa hannun Lives and Livelihoods Funds.
Wannan shirin bunƙasa noma ya na da lokacin da ya ke ƙarewa, wato tsawon wata uku.
Shi wannan shiri ne mai ɗauke da inganta noma, kiwo, noman rani.
Babban maƙasudin shirin dai shi ne a ƙara samun yalwar kayan abinci. Sai kuma abincin mai gina jiki.
“Muradin shirin dai shi ne a ga an rage yawan masu fama da fatara da talauci, ta hanyar bunƙasa abinci mai gina jiki a ɗaukacin jihar Kano baki ɗayan ta.
“Samun nasarar wannan shiri kuwa sai an haɗa noma da kiwo, kowanen sa an ba shi muhimmanci.” Inji Hamisu, Kodinetan KSADP na Kano.
Ya ce da ya ke ita Sasakawa ƙungiya ce mai matuƙar tasiri a Afrika, har da da Kungiyoyin Ƙasa-da-ƙasa na duniya, shekarun ta 36 kenan da kafuwa. To sai su ka haɗa kai da gwamnatin jihar Kano, don bunƙasa noman da ke kawo wa manomi kuɗi, da aka ware dala miliyan 19.3.
“Nauyin da aka ɗora wa ƙungiyar shi ne ta taimaka wa manoma 450,000 a faɗin jihar Kano, daga ƙananan hukumomi 44. Manoman da aka tallafa wa kuɗaɗen sun haɗa da manoman saralak, irin su shinkafa, masara, gero da sawa. Akwai kuma irin su tumatir, albasa da kabeji.
“Babban aikin mu shi ne bunƙasa wa waɗannan manoma harkokin su ta hanyar ƙara samun yalwar amfani noma da wadatar sa, ta hanyar ba su na’urorin fasaha, domin ganin a duk shekara su na samun aƙalla metrik tan 850,000 na abinci.
Hamisu ya ce wannan tsari ya bai wa mata muhimmanci, ta hanyar ganin su ma sun amfana a ƙarƙashin irin ta su gudummawar ta hanyoyin da su ke na su aikin.
Ya ƙara da cewa ta kai har mata na samun kuɗaɗen shiga bakin gwargwado. Sannan kuma ana ba su horo na koyon aiki, daga nan sai a ba su dukkan wani tallafin da ya dace ba tare da sun biya ba.
Hamisu ya ce ana samun matsaloli da kuma ƙalubale. Sai dai kuma ya ce dama irin sa ai don saboda su tunkari matsalolin domin su kawar da su.
Discussion about this post