Thersa Odu tsohuwar ma’aikaciyar gwamnati ce da ta yi ritaya. A yanzu ta rungumi harkar noma sau da ƙafa, a ɗaya daga cikin garuruwan da ke gefen Abuja. Kafin ta bar aikin gwamnati, ta rigaya ta ƙirƙiro tunanin fara noma. Amma kuma iyar nan tunanin ta ya tsaya a wancan lokacin, domin ba ta ma san abin da za ta riƙa nomawa ba.
To kada dai mu kai ku da nisa, Odu a yanzu ita ce Shugabar Gonar Odu Farms.
Thersa Odu mace ce wadda mijin ta ya mutu ya bar mata marayu biyar. Ta himmatu wajen harkokin noma da kuma kiwo.
Ta na da gonar noman ganyayen kayan miya. Ba a nan ta tsaya ba, ta na da ƙaton kandamin kiwon kifi, sannan kuma ta na kiwo kaji.
“Na fara aiki a Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama, kuma a can na yi ritaya da lokacin ritaya ta ya yi. Daga nan na yanke shawarar shiga harkar noma.
“Miji na ya rasu ina da ‘ya’ya biyar, daga nan sai na yi ritaya.
“Mun yi gamo-da-katarin samun yi mana horo a Kaduna, daidai lokacin da mu ka kusa ritaya. To daga nan sai na ƙara samun ƙwarin guiwar tsunduma harkokin noman kayan miya, wato hanyaye ina kaiwa manyan kantina. Daga nan kuma sai na tsunduma kiwon kaji.” Inji Odu, a tattaunawar ta da PREMIUM TIMES.
“To sai dai kuma ita wannan harka ta noma, akwai matsaloli da ƙalubale a cikin ta. Na shige ta a lokacin da ba ni ƙarfin jari. Don yawancin kuɗaɗen da na fara jalautawa ɗin, kuɗaɗen sallama ta daga aiki ne, wato garatuti.”
Odu ta ce saboda rashin ƙarfin jari, ma’aikatan ta ba su wuce biyar ba. Kuma albashin su dai ba laifi, akwai masu ɗaukar N30,000 a wata, har ma mai N60,000 a wata akwai.
“Sai dai a gaskiya ni ban ga wani ƙoƙarin da su ke yi min don haɓaka harkokin noma na ba. Ban sani ba shin albashin ne ya yi masu kaɗan, su ke raina abin da na ke ba su, ko kuwa dai yaran yanzu ne ba su son yin aikin wahala su samu kuɗi?”
Odu ta ƙara da cewa ta na kiwon ƙananan ‘yan tsaki, saboda ƙarancin kuɗaɗen jari.
“Kun ga ni ina so na ƙara ɗaukar ma’aikata, waɗanda su ka yi digiri a harkar nan. Amma saboda wurin nawa ba mai kyau ba ne, ba kowa zai so ya iya yin aiki a cikin wurin ba.”
Ta yi kukan rashin samun isasshen kayan feshin kashe ƙwari a gonar noman kayan miyar ta.
Odu ta ce a baya can a da za a iya samun kaji 3000 a gonar ta. Amma yanzu hakan ya zama tarihi.”
Ta ce ta na cikin Ƙungiyar Masu Kiwon Kani ta Najeriya, Reshen Abuja.
Kuma ta ce gonakin ta ba a wuri ɗaya su ke ba, a yankuna daban-daban, waɗanda idan aka haɗa yawan su to faɗin hekta biyu.
Discussion about this post