An gina titin Damaturu zuwa Biu cikin 1970, da nufin kusantar da al’umma mabambantan al’adu a wuri ɗaya, haɓɓaka tattalin arzikin yankin da kuma samar wa manoman yankin sauƙin zirga-zirga da safarar amfanin gona zuwa kasuwanni da sauƙaƙa hada-hada da harkokin yau da kullum.
Labarin nan wanda bai san halin da titin ke ciki a halin yanzu ba, zai ɗauka ko tatsuniya ce. Sai dai kuma maganar gaskiya, titin wanda a shekarun baya ya zama sanadin wanzuwar alheri, ci gaba, yalwa da bunƙasar manyan garuruwan biyu, a yanzu ya zama abin tausayi. Haka duk matafiyin da ya bi kan titin shi ma sai ya yi jigatar da zai zama abin tausayi. Hatta kuma motar da aka hau kan titin ita ma sai ta bigata, ko kuma ma ta kakare a can, a bar ta a daji.
Duwatsu da burji da yashin da ke kan titin a kullum su na shan gurza da tayoyin motoci, saboda babu kwalta.
Babu inda ya fi lalacewa kamar daga garin Maza zuwa Biu, idan an shiga Jihar Barno kenan, ta kai mutane irin su Salisu Ibrahim ta kai har sun yi sabo da bin hanyar. Ko kuma a ce sabo da jigata kan titin.
Tun Salisu ya na ƙorafin gyara titin, yanzu jikin sa ya yi sanyi, ganin ya shafe shekaru shida ya na karakaina a kan titin. Yanzu tsoro da fargabar sa, shi ne bai san yadda titin zai kasance nan gaba ba.
“Wato a gaskiya idan na kai shekaru 50 a duniya, zan daina aiki kan titin. Saboda babu inda ba ramu a kan kwalta ɗin.
“Mun riga mun shiga yanayin damina a yanzu. Motar mutum za ta iya kafewa wuri ɗaya, ya shafe kusan yini ya kasa gaba, ya kasa baya. Kai wani lokaci ma sai mota ta cakire tsawon kwanaki a wuri ɗaya, kuma a lalace.” Haka Salisu mai shekaru 47 ya bayyana wa wakilin mu, a lokacin da ya ke tuƙi ya na dukan ramu da motar sa.
Salisu ma cikin waɗanda su ka yi kwanan farin ciki, lokacin da a ranar 3 Ga Disamba, 2014 Ministan Ayyuka na lokacin, Mike Onolememen ya bada labarin cewa Gwamnatin Tarayya ta bayar da kwangilar sake gina lalataccen titin.
Shekaru 9 kenan bayan Mike ya shaida wa manema labarai a Fadar shugaban ƙasa labarin kwangilar, har yau titin ba a kammala shi ba.
Tun a cikin 2016 aka fara kai kayan aiki, irin su Katafila, taraktoci da sauran su, a kan titin, wanda aka gina shi tun cikin 1970. To rabon titin da ya sake jin gyara ya kai shekaru talatin ko fiye.
“Wannan gyaran da aka katse kwaltar ɗin dai bai yi mana daɗi ba. Da sun sani ma da an bar mana titin kamar yadda ya ke tun farko yadda su ka same shi.” Inji Salisu.
Ga Ƙoshi Ga Kwanan Yunwa: Ga Babbar Kasuwa A Biu, Amma Titin Zuwa Biyu Ba Daɗi:
Tsawon titin bai wuce kilomita 125, amma a haka ake bin sa zuwa gawurtacciyar kasuwar Biu.
An bada kwangilar gyaran titin ga kamfanin Messrs Fik Global Resources Ltd, cikin 2014.
An bada gyaran a kan naira biliyan 8.1. Bayan sa-toka-sa-katsi tsawon shekaru, har yau aikin ya tsaya. Kuma babban abin takaici, babu batun ci gaba da aikin a wannan shekarar, wataƙila ma har a wata ko wasu shekaru masu zuwa nan gaba.
Discussion about this post