Allah ya ƙaddara wasu maniyyatan Jihar Jigawa na da sauran shan ruwa a gaba, bayan da jirgin Max Air da ke ɗauke da su ya yi saukar gaggawa a filin jirgin Malam Aminu Kano da ke Kano, a ranar Laraba.
PREMIUM TIMES kafin nan ta bayar bayar da labarin yadda jirgin ya yi saukar gaggawa bayan walƙiya da tsawa sun jijjiga shi.
An tabbatar da cewa bayan saukar gaggawar ce aka saka maniyyatan cikin wani jirgin ya tashi da su.
Manajan Max Air da ke Kano, Bello Ramadan, ta tabbatar wa wakilin mu cewa jirgin wanda ke ɗauke da maniyyatan daga Jigawa ya sauka Kano ba shiri ne saboda wasu matsaloli daga injin jirgin.
Amma dai Bello bai bayyana wa wakilin mu kowace irin matsala ba ce. Ya dai ce an tanadar masu wani jirgin, wanda ya ɗauke su zuwa Saudi Arabiya tun a ranar Alhamis, ƙarfe 3 na yamma.
Shi kuwa Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa, Umar Labbo, ya shaida wa manema labarai cewa jirgin wanda ya kwashi maniyyata a lodi na biyu daga Jigawa, ya samu matsalar mai ne a daidai lokacin da ya shiga sararin samaniyar Kamaru. Daga nan ne ya juyo a sukwane zuwa Kano.
Labbo ya ce dukkan maniyyatan lafiyar su ƙalau, babu wanda ya samu ko ƙwarzane a jikin sa bayan sun sauka filin jirgin saman Malam Aminu Kano, da ke Kano.
PREMIUM TIMES ta gano cewa matuƙin jirgin ya zaɓi komawa Kano ne bayan malejin da ke nuna yawa ko ƙarancin mai ya tsaya cak, ya fara aiki tsawon awa uku cur ana darzaza tafiya a sararin samaniya.
Daga nan ne ya ji tsoron cewa sauran man da ya rage masa ba zai iya isa da shi har Jiddah ba. Daga nan ya karyo linzami, ya zabura zuwa Kano ya sukwane.
Tun da farko dai jirgin ya bar Filin Jirgin Saman Dutse ranar Laraba ƙarfe 4.45, tafiyar awa huɗu zuwa Jiddah, amma saboda rikicin Sudan sai jirage ke yin kewayen awa bakwai.
Discussion about this post