Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewa daga yanzu ba za a yarda wani maniyyaci ya wuce adadin kwanaki biyar a Madina, kafin ya zarce Makka ba.
Cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai, Musa Ubandawaki ya sa wa hannu, ya ƙara da cewa an fito da wannan sabon tsarin ne domin a rage cinkoson masu zuwa ziyara a Madina.
Ubandawaki ya ƙara da cewa hukumar su ta fara amfani da bin wannan tsari bayan ta tuntuɓi waɗanda ya kamata.
“An ƙirƙiro wannan tsarin ne bayan da aka yi kuka dangane da ɗimbin yawan ‘yan Najeriya a Madina,” inji shi.
Ya ƙara da cewa NAHCON ta fito da wannan tsarin ne domin idan ba a yi gaggawar fito da tsarin ba, to cinkoson ‘yan Najeriya a Madina zai iya fusatar da Gwamnatin Saudiyya har ta ladabtar da Najeriya.
Ya ce tilas ne a rage kwanakin da maniyyatan Najeriya a Saudiyya, saboda kauce wa fushin mahukuntan Saudiyya.
Ya ce yanzu duk duniya an san cewa tsarin aikin Hajji ya canja, saboda ci gaban zamani.
Aƙalla mutum 96,000 ne za su taki Arfa a bana daga Najeriya.
Tuni dai aka kwashi sama da maniyyata 30,000 daga cikin 96,000 daga Najeriya.
Discussion about this post