Aƙalla Alhazan Najeriya shida ne da suka halarci aikin Hajjin shekarar 2023 suka rasu a yayin gudanar da aikin, kamar yadda wani jami’in hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ya bayyana a Makka.
Shugaban kungiyar likitocin NAHCON, Usman Galadima ne ya bayyana haka a ranar Asabar a yayin wani taron hukumar a birnin Makkah.
Galadima, a cikin jawabinsa, ya ce jihohin Osun da Kaduna sun samu mace-mace guda biyu kowanne, yayin da jihar Filato ta samu mutum daya.
Don magance yawan mace-macen, Galadima ya yi kira da a karfafa aikin tantance masu niyyar zuwa aikin hajji kafin aikin hajji. Ya kara da cewa akwai bukatar a rika hana wadanda ake ganin ba su dace da tafiya ba domin guje wa irin waɗannan matsaloli da ake fama da su, kamar a wannan shekara.
“Abin da muke kira a kai shi ne a karfafa aikin tantance maniyyata kafin aikin hajji. Wanda ba shi cikin koshin lafiya ko kuma yana da wata matsala ko kuma ma tsofar sa zai iya hana shi gudanar da aikin yadda ya kamata sai a rika dakatar da su.
” An samu mutum 30 dake fama da taɓuwar hankali wanda yanzu haka suna kwance a na duba su. Ana sa ran idan suka samu sauki su iya gudanar da ayyukan Hajjin su. Sannan kuma mata biyu sun yi ɓari, wata kuma ta haifi bakwani ta hanyar yi mata aiki.
Ya bayyana cewa an yanke wa wani mutum daya kafa saboda matsalar ciwon suga. Sannan kuma da wasu tsoffi 8 da suka matsalar karaya a lokacin aikin Hajji.
A jawabinsa na bude taron, shugaban hukumar Zikrullah Hassan ya ce duk dan Najeriya da yake da ingantaccen bizar aikin hajjin 2023 an dauke shi zuwa kasar Saudiyya.
Sama da mahajjata miliyan biyu ne ake sa ran za su yi aikin hajjin na shekarar 2023.
Discussion about this post