Jigilar maniyyata daga Najeriya zuwa Saudi Arabiya daga Najeriya zai karu nan da sa’o’i kadan. An shafe kwanaki 27 ana jigilar maniyyata inda akalla jirage 170 zuwa yanzu sun tashi da sauka a filayen saukar jiragen sama na Jeddah da Madina da mahajjatan Najeriya sama da dubu 71,000 kuma har yanzu kokarin ganin an kammala kwasar sauran.
Shugaban hukumar NAHCON, Zikrullah Hassan, a madadin hukumar gudanarwar hukumar, yana taya alhazan Najeriyar da suka isa kasar Saudiyya da kuma sauran ‘yan Najeriya fatan za a gudanar da aikin Hajj Karbabbe.
Hukuma ta ce zuwa ranar Asabar mai zuwa za a kammala jigilar maniyyatan gaba dayan su.
Za a gudanar da hawan Arfat ranar Talata mai zuwa, sannan a gudanar da babban Sallah ranar Laraba.
Bayan haka, Zikirullah ya nuna rashin jin dadin sa ga maniyyatan da ba su samu damar zuwa aikin Hajji na baban ba, cewa su dauki hakan a matsayin Kaddara. ” Shi zuwa aikin Hajji kiran Allah ne, duk yadda kaso idan lokaci bai yi ba ba za ka tafi ba. Su hakuri su kuma kyautata niyyar su sannan su yi imani da kaddarar haka.
Discussion about this post