Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal na zargin tsohon gwamnan jihar Bello Matawalle da sace wasu motocin gwamnati a lokacin da yake sallama da gidan gwamnati.
Gwamna Lawal na PDP ya kada Matawalle a zaben gwamnan da aka yi ranar 18 ga Maris.
A wata sanarwa dake dauke da sa hannun mai taimakawa gwamna Lawal kan harkokin yada labarai Sulaiman Bala- Idris, Lawal na zargin Matawalle da sace wadannan motoci ba tare da ya yi la’akari da hukuncin dake tattare da yin hakan ba.
A wani Shirin da gidan rediyon Vision FM dake garin Gusau ya yi ranar Laraba Lawal ya ce Matawalle ya kwashe motoci, na’urar sanyay ɗaki , talabijin da dai sauran kayan dake cikin fadar gwamnati.
Jam’iyyar APC ta ce ana yi wa tsohon gwamnan bita da Ƙulli da Sharri ne, amma babu wani abu mai kama da abinda da ake zargin ya aikata ya aikata.
Bala-Idris ya cigaba da cewa kokarin kare Matawalle da APC ta ke yi yanzu, naɗe tabarmar kunya ce. Amma ay Matawalle ya wawushe dukiyar mutanen Zamfara.
“Gwamnati a shirye take domin farfado da jihar Zamfara musamman ta fannin dawo da dukiyan gwamnati da aka sace.
“Muna da takardu dake dauke da bayanan dake yadda Matawalle ya yi sama da fadi da kudade da ƙadarorin gwamnati.
“Matawalle ya bada kwangilan naira biliyan N1,149,800,000.00 domin siyo motocin da za a raba wa wasu manyan jami’an gwamnati da ma’aikatu a jihar.
“Kamfanin Hafkhad Properties and Facilities Management Nig. LTD ne aka ba wannan kwangila domin siyo motoci kiran Toyota Lexus VIP Bullet Proof 2021 Model; Toyota Land Cruiser VIP Bullet Proof 2021 Model; Toyota Prado V6 2021 Model; Toyota Prado V4 2021 Model; Peugeot 2021 Model; Toyota Hilux 2021 Model; Toyota Land Cruiser Bullet Proof 2021; and Toyota Lexus 2021 Model.
“ Kuma a ranar 4 ga Oktoba 2021 Matawalle ya biya Kamfanin MUSACO naira miliyan 484, 512, 500.00 domin siyo motoci bakwai kirar Prado Jeep da Land Cruiser sannan ya sake biyan Naira miliyan 228,830,000 domin siyo motoci bakwai kiran Toyota Hilux.
Matawalle na daga cikin gwamnonin da tun kafin su sauka daga mulkin jihohin su hukumar EFCC suka kyallara fitilar su a kan su, cewa su kwana da shirin fuskantar binciken hukumar.
Discussion about this post