Gwamnan Kano Abba Yusuf ya umarci a rusa ginegine da aka yi su bisa filayen gwamnati da gwamnatin da ta shuɗe ta raba wa ƴan uwa da abokan arziki.
Tun kafin a rantsar da sabon gwamna Abba Yusuf, ya rika gargaɗin waɗanda suka yi gine-gine a filayen gwamnati da tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya raba su.
Ginin da aka soma rusa wa ginene bene mai hawa uku dauke da shaguna 90.
Gwamna Yususf da kwamishinan ƴan sandan jihar Mohammed Gumel da suka yi tsaye a wurin aikin har sai da aka gama.
Ginin na rukunin gidajen gwamnati dake Nasarawa ne.
Discussion about this post