Gwamnatin jihar Kano ta hana lika fastoci a gine-gine a fadin jihar, na gwamnati ne ko kuma wadanda ba na gwamnati ba.
A wata sanarwa wanda sakataren yada labarai na gwamna Abba, Bature Tofa ya saka wa hannu, gwamnati za ta kungiyar duba gari musamman don hukunta wanda ya saba dokar.
Tofa ya ce gwamnati ta dauki wannan domin tsaftace garin ganin like liken fosta irin haka ya lalata cikin garin gaba dayan sa.
Sanarwa ta yi kira ga ‘yan siyasa da hukumomi da su rika amfani allunan tallace-tallace ko allunan tallace -tallacen dake amfani da wutan lantarki domin tallata hajojin su gudun kada a saba doka.
” A dalilin haka, gwamna Yusuf ya umarci hukumar kashe gobara ta jihar da tabi ko’ina ta cire duk wani Fosta da ta gani like a ginegineb jihar.
Discussion about this post