Gwamnatin tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ta yi kurin kashe sama da Naira biliyan 20 wajen biyan kudin makaranta da kula da dalibai 111,687 ‘yan asalin jihar dake karatun digiri a kasashen waje 14.
Gwamnatin ta kuma biya kudin makarantar dalibai ‘yan jihar dake karanta darasin shari’a a jami’o’I biyar masu zaman kansu da wasu jami’o’in kasar nan daga watan Yuni 2015 zuwa Maris 2023.
Kwamishinan yada labarai na tsohon gwamnan Muhammad Garba ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai a garin Kano ranar Litini.
Kwamishinan ya maida martani ne game da korafin da gwamnati mai ci ta yi cewa wai gwamnatin Ganduje bata tabuka komai ba wajen biyan kudin makarantun dalibai yan asalin jihar dake karatu a kasashen waje.
Garba ya ce gwamnatin Ganduje ta biya wa daliban jihar dake karatu a kasashen India, Malaysia, Egypt, Cyprus, China, Turkey, Uganda, United Kingdom, Togo, Ireland, Gambia da Ukraine da wasu jami’o’in dake Najeriya kudin makaranta, guziri, kudin jirgi da dai sauran su.
Ya Kuma ce gwamnati tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar Faransa sun biya karatun digirin digir-gir-gir na malaman jami’o’I 50 dake aiki a jami’o’in dake jihar da suka karanta darasin French a kasar Faransa.
Garba ya musanta zarge zargen da wannan gwamnati ta yi akan gwamnatin Ganduje yana mai yin karin bayani cewa, duk da cewa gwamnatin Ganduje ta iske basussuka a lokacin da ta hau mulki, duk da haka ta iya biayn su kusan duka sannan ta yi kari akan abin da ta samu a baya.
Sai dai kuma, Dalibai da dama wadanda ke karatu a kasahen waje, sun shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA, cewa gwamnatin da ta wuce ta barsu cikin halin ha’ula’i a makarantun su. Sun bayyana cewa a wasu lokuttan ma sai da aka dakatar dasu karatun zango guda saboda gwamnatin a lokacin bata iya biya musu kudin makaranta ba a kasashen da suke.
Discussion about this post