Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya dakatar da ma’aikata akalla 10,800 da aka dauka aiki a lokacin gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.
A ranar Litinin, Akanta Janar na jihar, Abdulkadir Abdulsalam, ya ce ma’aikatan da abin ya shafa na daukarwar an ɗauke su ne ba bisa ka’ida ba a wancan lokacin.
Ya ce ba za a biya waɗannan ma’aikata ko sisi ba a watan Yuni, kada ma su sa ran samun albashi.
” Waɗannan ma’aikata an ɗauke su ne ba bisa ƙa’ida ba, a dalilin haka kuma gwamna ya ce a dakatar da su da kuma albashin su gaba ɗaya sai an kammala bincike akan harkallar ɗaukan su aiki.
” An gano cewa da yawa daga cikin waɗanda aka ɗauka ma ƴaƴan manya ne ba su ma ko gama karatu ba aka sakalasu cikin aikin gwamnati su rika karbar albashi, babu aikin fari bare na baki, sannan kuma wasu da takardun boge suka shiga aikin.
Tuni gwamnati ta nada kwamiti domin su duba yadda aka ɗauki waɗannan mutane aiki da duk abinda ya kama a duba. Bayan haka ne za a iya maida su aiki nan gaba
Gwamnatin Ganduje ta yi rubibin arigizon sabbin ma’aikata gab da zata yi sallama da gidan gwamnati, wanda da dama daga cikin su ana zargin ba su da takardun kwarai.
Discussion about this post