Hukumar tsaro ta SSS a ranar Alhamis a Abuja ta gargadi jama’a da su yi taka-tsan-tsan da hare-haren ta’addanci a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke shirin gudanar da bukukuwan Sallah Eid-el-Kabir.
Kakakin hukumar, Peter Afunanya, ya bayyana cewa, rahotannin da suka samu sun nuna shirin kai hari kan wuraren ibada da wuraren shakatawa kafin da kuma lokacin bukukuwan.
A cewarsa, rahotannin sun tabbatar da kama wasu bama-baman daga wasu da ake zargin ƴan ta’adda ne a yayin wani aikin samar da tsaro na hadin gwiwa da wasu jami’an tsaro da aka yi.
Afunanya ya kara da cewa hukumar ta kai samame a maboyar ‘yan ta’adda a jihohin Kogi da Nasarawa a ranar Litinin da ta gabata tare da hadin gwiwar rundunar sojojin Najeriya da jami’an ‘yan sanda.
Afunanya ya kara da cewa, samamen da aka kai a hanyar Abuja zuwa Keffi jihar Nasarawa ya kai ga kama wani ƙasurgimin dillalin bindigogi da harsasai.
Ya kuma bayyana cewa, rundunar hadin guiwar jami’an tsaro sun kai samame maboyar wani da ya yi ƙaurin suna wajen arcewa daga kurkuku kuma fitaccen gogarman ɗan kungiyar ‘yan ta’adda a Ejule, karamar hukumar Ofu a jihar Kogi ranar Alhamis.
A lokacin kai wannan samame an yi artabi da batakashi tsakanin jami’an tsaro da ƴan bindigan, kuma Allah ya ba jami’an tsaro sa’an kashe ɗan bindigan, sai dai wasu daga cikin yaran sa sun arce da suka ji wuta.
Afunanya ya kuma bayyana cewa, kayayyakin da aka kwato a wurin sun hada da bindiga kirar AK47 guda daya dauke da mujallu uku cikakku, bindigogi kirar hannu guda shida, wayoyi biyu da kuma layu.
Ya yi kira ga masu gidajen mai, wuraren Ibada, shakatawa, kasuwanni, kantuna da su saka ido matuka da kuma jawo hankalin jami’an tsaro idan ba su yarda da wulƙawar wani ba ko wasu mutane a wuraren su ba
Discussion about this post