Sabon Kakakin Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Tajuddeen Abbas, ya bayyana cewa nasarar sa ta zama Kakaki na Majalisa ta 10, ya kunyata masu surutai da gulmar cewa ba zai iya yin nasara ba.
Da ya ke magana da manema labarai ranar Talata a Fadar Shugaban Ƙasa, ya ce akwai mutanen da ke cewa shi Abbas ɗin ba shi da magoya baya, saboda wai jam’iyya ce ta ƙaƙaba shi tilas.
Cikin ‘yan rakiyar Abbas zuwa Fadar Shugaban Ƙasa akwai Mataimakin Kakakin Majalisa, Ben Kalu, inda su ka je domin kai caffa ga Shugaba Bola Tinubu, bayan yin nasarar zaɓen su na shugabannin majalisa.
Tun cikin watan Mayu Tinubu ya nuna cewa Tajuddeen Abbas da Ben Kalu ya ke goyon baya, kamar yadda ita ma APC ta bayyana cewa ta na goyon bayan su biyun.
Abbas ya samu ƙuri’u 353, yayin da abokin gamayyar sa Idris Wase, wanda shi ne tsohon Mataimakin Kakakin Majalisa, ya tashi da ƙuri’u uku kacal. Haka shi ma Aminu Jaji ukun ya samu.
Kusan dukkan mambobi na APC da sauran na jam’iyyun adawa, duk Abbas su ka zaɓa.
“To yanzu dai ai mutane sun ga irin goyon bayan da mu ke da shi na yawan waɗanda ke tare da mu. Kenan mun kunyata masu ganin cewa jam’iyyar APC ce ta ƙaƙaba mu kan muƙami, wai ba mu da masu goyon bayan mu,” inji Abbas.
Ya ƙara da cewa wasu ‘yan takarar ma sun yi amfani da soshiyal midiya su na farfaganda baddala gaskiya su na maida ta ƙarya a lokacin kamfen ɗin su, don kawai su nuna cewa Abbas ɗin ba shi da magoya baya.
“Amma Allah cikin ikon sa, a yau jama’a sun ga irin goyon bayan da mu ke da shi daga hannun mambobin Majalisa.” Inji Abbas.
Abbas ya ƙara da cewa ba za su taɓa zama su shantake su noma ‘yan amshin-Shata ba.
Ya ce duk inda ya kamata za su tafi tare da gwamnati, to za su tafi tare. Inda kuma su ka ga za su nuna rashin amincewa a inda ya dace, to ba za su yi wa gwamnati amshin-shata ba.
Shi kuwa Ben Kalu cewa ya yi za su taimaka wa Tinubu ya kai ga nasara bisa ga kyawawan manufofin da ya ɗauki aniyar aiwatarwa.
Discussion about this post