Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) ta bayyana cewa ta kama dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele.
DSS sun kama shi, ba da daɗewa ba bayan Gwamnatin Tarayya ta bayar da sanarwar dakatar da shi.
Sanarwar da damƙe Emefiele ta fito daga bakin Kakakin Yaɗa Labaran SSS, Peter Afunanya, a cikin wata sanarwar manema labarai da ya raba, ya aiko wa PREMIUM TIMES.
“Lallai dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele na hannun mu. Ya na tsare ne aka yi masa wasu tambayoyi dangane da binciken da ake yi kan sa.” Haka dai Afunanya ya rattaba a ciki sanarwar da ya aiko wa PREMIUM TIMES.
Idan ba a manta ba, cikin watan Disamba, 2022 SSS sun nemi kama shi domin zargin ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda, amma kotu ta hana su, saboda rashin ƙwaƙƙwarar shaida.
PREMIUM TIMES Hausa ta bada labaein Tinubu ya dakatar da Emefiele, gogarman da ya yi wa Naira fentin zabibi, bayan dala ta kai Naira 750 a ƙarƙashin sa.
Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin dakatar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele cikin gaggawa.
Dakatarwar ta zo cikin mako biyu bayan kama ragamar mulkin Najeriya da Tinubu ya yi daga hannun tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.
Datakar da Emefiele na cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ya fitar ranar Juma’a, da dare.
Dakatar da Gwamnan CBN ya biyo bayan wani gagarimin bincike da ake kan yi a ofishin sa da kuma shirin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.
An umarci Emefiele ya gaggauta damƙa kayan aiki na ofishin sa a hannun Mataimakin Gwamnan CBN Sashen Gudanarwa, wanda zai ci gaba da zama Gwamnan CBN na Riƙo, kafin a kammala bincike.
Dakataccen gwamnan na CBN ya fara aikin gwamnan bankin ne tun cikin 2014, bayan da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya dakatar da Sanusi Lamiɗo Sanusi daga shugabancin CBN.
Kafin naɗin sa gwamnan CBN, Emefiele shi ne Babban Daraktan Bankin ZENITH.
Tun bayan hawan sa gwamnan CBN, Emefiele ya Sha suka sosai daga ‘yan Najeriya, musamman saboda rashin iya tafiyar da tattalin arzikin ƙasar nan da ya kasa taɓuka komai a kai. Ga kuma tsare-tsaren da riƙa fitowa da su waɗanda ba su zame wa ƙasar nan alheri ba.
A zamanin sa darajar Naira ta yi lalacewar da har ta kai Naira 750 ke yi dala 1 a kasuwar ‘yan canji, a farashin gwamnati kuwa Naira 469.50 ke yin dala 1.
Akwai kuma matsalar yadda CBN ya kasa yin komai ga shi har malejin tsadar rayuwa ya kai kashi 22.2 a cikin Mayu, kamar yadda Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta fitar.
Emefiele an zarge shi da shirya gidogar da ta haifar da canjin launin Naira, lamarin da ya jefa baki ɗayan ƙasar nan cikin masifa da ruɗani.
Baya ga zargin sa da laifin ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda, sannan kuma ya bai wa Gwamnatin Buhari ramcen Naira tiriliyan 23.7 na asusun CBN, ba tare da ya tuntuɓi Majalisar Dattawa da ta Tarayya ba.
Cikin Disamba SSS sun nemi kotu ta ba su iznin damƙe shi don a bincike shi kan zargin ɗaure wa ‘yan ta’adda gindi, amma Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta hana, bisa dalilin rashin ƙwaƙƙwarar hujja.
Emefiele ya sha caccaka lokacin da ya yi katsagallin yunƙurin fitowa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC.
Kusan sau huɗu PREMIUM TIMES na nuna wa duniya matsayar ta kan Emefiele cewa a gaggauta tsige shi, kuma a garƙame shi a kurkuku, amma gwamnatin Buhari ba ta yi komai a kai ba.
Discussion about this post