Kafin mu soma batu a kan wannan al’amari ya kamata duk mai bibiyar kudurorin gwamnati a kan harkar ilimi musamman na manyan makarantu, ya san a kwai shirin da gwamnatin baya ta yi a kudundune, duk da kokarin wayar da kai da a ake, mutane sun gaza ganin muhimmancin wannan batu.
Abun da yake bai bayyana sosai ba, a cikin rikicin yan ASUU da tsohuwar Gwamnatin Buhari ya hada da yunkurin da gwamnatin tayi na cire tallafi a kan harkar ilimi manyan makarantu, ta yadda za a fito da tsarin biyan tuition fee da kuma Karin biyan wasu kudden makarantar.
In mun tuna baya a jawabin tsohon shugaban kasa Buhari a wajen bayanin kasafin kudin wannan shekarar, yace daga wannan shekara, gwamnati baza ta ci gaba da daukan dukkannin bukatun manyan makarantun ta ba. Koma me ke faruwa, arewacin Nijeriya ne a baya.
Me muka fahimta game wa wannan doka ta bawa dalibai bashin kudin karatu?
Wannan Doka wadda Tsohon Kakakin Majalissar-Tarrayya kuma yanzu shugaban ma’aikatan fadar Shugaban Kasa, Hon. Femi Gbajabiamila ya kai kudurin gaban Majalissar-Tarayya “Student Loan (Access to Higher Education) Bill”, wadda a yanzu ya zama doka bayan samun sahalewar Shugaba Bola Ahmed Tunubu.
Ita wannan doka ta samar da kirkirar da wani Asusu domin Ilimin Yan Nijeriya (Nigerian Educational Fund) wanda zai zama a babban bankin Nijeriya (CBN), wanda duk wani dalibin da ya cika sharuddan karbar wannan bashin, babban Bankin-Kasa (CBN) zai bashi ta hannun bankunan kasuwanci na kasa, wato Commercial Banks.
A Sashi na 3 a cikin wanna doka (Student Loan Act, 2023) yace “wannan bashi da a ka bayyan a cikin wannan doka za a bayar ne kawai da dalibai domin su biya TUITION fees kadai”.
Amma fa, kundin tsarin mulkin Nijeria (1999 Constitution as Amended) a constitutional matter a kasha na biyu (Chapter 2) ya haramta biyan tuition fees ga duk wani dan kasa, “a tanaje tanejan wannan sashi, babu wata makaranta mallakar gwamnati da a ka amincewa da ta karbi TUITION Fees a kan duk wani dan kasar nan”
Wannan kadai zai nuna cewa, gwamnati zata bijoro da biyan kudin TUTION Fees a makarantun mu, kuma su bada bashi don a biya su da shi, kudin zai koma dai wurin su, sannan ga nauyin bashi a kan daliban. Ba wai za a bada bashin bane don biyan kudin registration fees, kudin abinci da sauran wahalhalun da dalibai keyi ba. Abu mafi muhimman ci shine, ‘Yan Nijeriya su sake sauraron sabuwar dokar da za tilasta biyan kudin TUITION FEES gay an kasa.
Abu na biyu, da shima in ba a yi da gaske ba, zai targada karatun arewacin Nijeriya shine, ka’idodin da a ka sanya domin karbar wannan bashin.
Duk dalibin da zai karbi wannan bashin, sai dalibi ya kawo masu tsaya masa wato guarantor guda biyu, daya ya kasance ma’aikacin gwamnati mai matakin albashin na 12 da kuma Lauya, wanda ke da kwarewar shekara goma ko ma’aikacin shari’a.
Wannan tsari a farko ba komai zai kawo ba sai hana yaran talakawa samun damar karatun gaba da sakandire. Samun cika wannan ka’idodin kowa yasan zai yi wahala cikawa, musamman ga yayan talakawan da ke zaune a karkara, komai niyar su, ilimin su da fasahar su da nacin su na son karatun.
Anyi kiyasin cewa wannan tsarin, za a iya kasha sama da Naira Tiriliyan Daya domin bayar da wanna bashi a duk shekara, wannan kudin in har gwmanti na da shi da kuma bada sukunin bayadda da bashi, ya isa koma yafi abin da ake bukata domin bawa yan kasa tallafin yin karatun a jami’oi ko makarantun gaba da sakandare.
In har wannan wannan doka ta soma aiki, kuma gwamnati tayi nasarar gyaran kundin tsarin mulki ta wajen kirkiro da biyan tuition fees a manyan makarantun kasar, to fa mutanen Arewacin Nijeriya wanda dama suke da tasgaron ilimi wannan abun zai shafa.
Na farko, daman akwai tazara mai dinbin yawa a wajen bunkasar ilimi musamman ma nag aba da sakandire tsakanin arewaci da kudancin wannan kasa. Wannan ba komai zai harfar ba sai kara wannan tazara da gibi, kullun arewa za ta kasance a baya duk da gudunmawar da suke bayar wa a siyasance. Wannan ci baya ba kawai ilimi ba, har ma a duk fannoni da cigaba.
Na biyu, karancin aikin yi a wannan yankin musamman ma aiyukan da suka jibinci karatun boko, zai yi wahala mutane su tsunduma wajen karbar wannan bashin, domin rashin tabbas na samun aikin da za su biya wannan bashin.
Na uku, kamar yadda na fada a baya, abu ne mai wuya ga mutanen mu na karkara su iya cike wannan ka’ida, wanda a takaice wannan wani tsari ne da hana yaran mu na arewacin wannan kasa, cika wannan sharudda, wannan ba karamin kalubale bane wajen ci gaban wannan yankin.
Ya kamata mu sani cewa, mummnan yanayin da wanna yankin ya shiga na rashin tsaro da karfin talauci duka fa ya ta’allaka ne da rashin ingantance ilimi a wannan yankin.
Allah ya kyauta.
alhajilallah@gmail.com; Text: +234 8025 951609
Discussion about this post