Gwamnan jihar Zamfara, Daula Lawal ya kori duk manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnatin jihar Zamfara.
Fatattakar bai tsaya ga manyan sakatarori ba, har da duka wani hakimi ko dagaci da tsohon gwamna Bello Matawalle ya naɗa.
Gwamnatin jihar ta ce matakin na daya daga cikin sauye-sauyen da ta fara yi na gyara yadda Matawalle ya yi wujiwuji da dukiyar jihar.
Sakataren gwamnatin jihar, Abubakar Nakwada, a wata ganawa da manema labarai da ya yi a Gusau ranar Talata, ya ce gwamnatin da ta shude ta yi barna da bashi misaltuwa ga tattalin arzikin jihar.
Sakatare Nakwada ya ce dukkan gundumomin da aka kirkira a watan Disamba na 2022 an rusa su, sannan kuma duk wani babban sakatare da aka naɗa da aka ɗora bayan babban zaben 2023, shima ya tattara komatsan sa ya kara ga ba.
” Nan ba da daɗewa ba za a kawo sauye sauye masu ma’ana a ma’aikatun gwamnatin jihar da za su rahe ɓarnatar da kuɗi da ake yi.
Saboda tsananin rashin kan gado da kwamacala da aka rika tafka wa, gwamnatin Matawalle ta kashe Naira biliyan 50 wajen gudanar da ayyuka a gidan gwamnati wadanda ba su da wani tasiri na ci gaba a jihar.
Mene amfanin kashe irin waɗannan kuɗaɗe, bayan ga abin da za a yi da su mutanen jihar su ƙaru. Kuma idan ka shiga gidan gwamnatin ma, ba zaka ce ga abinda aka yi da su ba.
Sannan gwamnatin ta kashe biliyoyin naira wajen siyan motocin alfarma na gwamnati da wannan gwamnati bata gaji ko ɗaya ba.
Discussion about this post