Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa ba tare da wani ɓata lokaci ba.
Cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Fadar Shugaban Ƙasa, Willie Bassey ya fitar ba da daɗewa ba, an umarci Bawa ya gaggauta damƙa ragamar aiki a hannun Daraktan Ayyuka na EFCC.
Sanarwar ta ce an dakatar da Bawa har zuwa lokacin da za a kammala binciken zarge-zargen da ake yi masa.
Bawa wanda ya karɓi ragamar EFCC daga hannun Ibrahim Magu, shi ma ya yi irin fitar da Magu ya yi wa EFCC.
Tarihi ya nuna babu wani shugaban EFCC da ya taɓa kammala wa’adin sa ya sauka salum-alum, duk cire su aka riƙa yi.
An cire Nuhu Ribadu, haka ita ma Farida Waziri da Ibrahim Lamurde duk cire su aka yi.
Discussion about this post