Asari Dokubo ya bayyana cewa dalilin aikin samar da tsaro da ya saka yan barandan sa su yi a yankin jihar Neja ne ya sa aka samu tsaro a titin Abuja- Kaduna.
Hakan yana kunshe ne a jawaban da ya yi lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida bayan ganawa da shugaban kasa, Bola Tinubu a fadar gwamnati.
Asari ya ce Sojojin Najeriya ba su amfani kasar nan da komai ba sai hassada da mugunta. ” Bani da irin makaman da suke da shi amma saboda son kai da son tara dukiya, sun ki su yi abin da ya kamata su yi don kawo karshen ta’addanci a kasar nan.
” Wai sai ka ga sojoji makil da zakakuman kayan yaki na zamani a cikin motocin yaki na zamani, sai wasu tarin mutanen da ba su da komai sai tarkacen bindigogi, wai sai su fatattake su, su koma sojojin sai su bar musu motocin cike makil da kayan yaki su gudu. Kawai sun kai musu kayan yaki sun gudu.
” Ina tabbatar muku da cewa karkashin mulkin Tinubu za a ga canjin da ba a taba gani ba a kasar nan. Saboda shi mutum ne da ya san abinda ya kamata kuma ya kware wajen iya mulkin jama’a.
” Ni dinnan da kuke gani wallahi zai iya shiga gaba a harbe ni saboda Tinubu. Kuma ku saurare ni da kyau, Wallahi Tinubu ba zai ba mu kunya ba. Za a yaba masa irin wanda ba a taba yaba wa wani shugaba ba.
Sojojin Najeriya ne gaggan ɓarayin ɗanyen mai a Neja Delta
Gazagurun tsohon ɗan tawaye, Asari Dokubo, ya ce Sojojin Ƙasa da Sojojin Ruwan Najeriya ne manyan ɓarayin ɗanyen mai a Neja Delta.
Ansari ya yi wannan kakkausan zargi ranar Juma’a, lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu.
Ya ce fadar ne domin ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
“Sojojin Najeriya na Ƙasa da na Ruwa ne manyan ɓarayin ɗanyen mai a yankin Neja Delta. Su na firgita jami’an Sibil Defens waɗanda su ne ke tsaron wuraren ɗanyen mai. Ta kai ma kai tsaye su ke ɗaura bututu su riƙa zuƙa daga famfon ɗanyen mai.
“Abin da ke faruwa tsawon shekaru takwas kenan ya wuce hankali a duniyar nan. Babu inda aka taɓa yin gagarimar satar ɗanyen mai irin wannan ba a duniya.” Cewar sa.
“Sojojin Sama da na Ƙasa da aka tura don su samar da tsaro, su ne satar ɗanye mai har ta kai sun kafa wuraren tace mai. Haka kuma wannan laifi ne babba.
“Muhallin yankin na ci gaba da gurɓata. Kuma sojojin ƙasa da na ruwa su ne masu aikata wannan babban laifi.
Akwai wasu hatsabiban kwamandojin soja waɗanda ke sahun gaba wajen satar mai.
Ya ce amma yanzu zuwan Bola Tinubu da kuma ƙwarin guiwar da sabon shugaban ya ba shi, za a kakkaɓe sace-sacen ɗanyen mai a Neja Delta.
“Akwai wasu manya a Abuja masu hannu a satar mai. Amma zamanin Tinubu duk za a damƙe su, a maka kurkukun Kuje.”
Discussion about this post