Mazaunan kauyen Gabchyari dake karamar hukumar Darazo a jihar Bauchi sun bayyana cewa makarantun sakandare da firamare da suke da su a kauyen suna da dalibai 350 amma malamai uku ne kacal ke koyarwa a makarantun.
Mazaunan kauyen sun ce rashin malamai a makarantun yasa yaran kauyen ba su zuwa makaranta sai yawon banza a cikin gari.
Wani mazaunin kauyen Isa Ibrahim ya yi kira ga gwamnati da ta karo malamai domin rage yawan yaran da basu zuwa makaranta.
Shima Yahaya Adamu ya yi kira ga gwamnati da ta gyara makarantun domin dslibai su samu wurin zuwa su yi karatu.
Adamu ya ce daga ciki ajujuwa shida dake makarantar biyu ne kadai ake amfani da su.
Ya Kuma ce rashin tsaftacaccen ruwa na daga cikin matsalolin dake hana iyaye tura ‘ya’yan makaranta sanna da nuna halin ko in kula da iyayen ke nunawa.
“Rashin ruwa na hana yara zuwa makaranta domin sukan yi tafiya mai tsawo neman ruwan da zasu sha.
Wani Malami a makarantar, Abdullahi Muhammad ya ce a sashen sakandare malamai biyu ne kacal ke karantar da dalibai, malami daya kuma a fannin Firamare.
“Wasu lokuta iyaye kan tambaye mu malamai cewa menene muke koya wa yara gashi bamu da yawa.
“Zuwa yanzu muna da malami daya da shine Shugaban makarantar firamare dake da dalibai sama da 200 sannan Kuma yana koyarwa a a sashen sakandare dake da dalibai 150.
“ Sau da yawa ni da malamin da muke koyarwa a sakandare mukan koma sashen firamare mu koyar da dalibai.
Discussion about this post