A ranar da aka dakatar da Shugaban EFCC, Abdulrashid Bawa, washegari SSS sun yi awon-gaba da shi, kuma har yanzu ya can a tsare.
SSS sun tsare Bawa bayan Tinubu ya dakatar da shi.
A yanzu haka dai dakataccen Shugaban EFCC, Abdulrashid Bawa ya kwana ofishin SSS, bayan amsa gayyatar da aka yi masa.
SSS sun gayyace shi jim kaɗan bayan sanar da dakatar da shi da Shugaba Bola Tinubu ya yi.
Kamun tsare Bawa ya zo ne kwanaki uku bayan SSS sun tsare Gwamnan Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, wanda Tinubu ya dakatar a makon da ya gabata.
Gayyata da tsare Bawa na daga cikin binciken sa da aka fara, dangane da zargin sa da harƙalla, kamar yadda sanarwar dakatar da shi ta ƙunsa.
Kakakin SSS Peter Afunanya ne ya tabbatar da gayyatar da su ka yi wa Bawa da kuma tsare shin da aka yi, a sanarwar da ya fitar cikin shafin sa na Tiwita ƙarfe 10.48 na dare.
Dakatar da Bawa ya zo mako biyu bayan da aka samu rashin jituwa tsakanin EFCC da SSS a Legas, kwana ɗaya bayan rantsar da Tinubu.
Rikici tsakanin SSS da EFCC ya ɓarke ranar 30 Ga Mayu, yayin da SSS su ka tare duk wata hanya da EFCC za su bi su shiga ofishin su na Legas, har kusan tsawon yini ɗaya.
Sai da ta kai Shugaba Tinubu ya sa baki, kuma ya hore su su ka yin aiki kafaɗa da kafaɗa sannan lamarin ya saisaita.
Siyasar Cire Ribadu Daga EFCC:
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo ya naɗa Nuhu Ribadu shugaban EFCC, a 2003, kuma tsohon Shugaban Ƙasa Musa ‘Yar’Adua ya cire shi a ranar 27 Ga Desamba, 2007.
An tura shi NIPSS da ke Kuru, domin ƙara karatu, amma a ranar yaye ɗalibai SSS su ka fitar da shi da ƙarfin tsiya.
Daga baya an rage masa muƙami zuwa Mataimakin Sufeto Janar.
An cire Ribadu lokacin da ya tasa Tsohon Gwamnan Delta, James Ebori a gaba. Ebori makusancin Yar’adua ne a lokacin.
Masana shari’a da kuma masu sharhi na cewa daga cire Nuhu Ribadu aka fara saka siyasa a sha’anin EFCC.
Ibrahim Lamorde: Desamba 2007 Zuwa 2008:
Wannan lokaci Lamorde Shugaban Riƙo ya kasance.
Farida Waziri: 2008 Zuwa 2011:
Fareda ta samu saɓani da Gwamnatin Yar’adua, saboda zarge-zargen da aka yi mata.
An cire ta aka naɗa Lamorde a karo na biyu.
Lamorde: Daga 2011 Zuwa 2015:
Sanatoci sun kafa masa kwamitin bincike, bayan an zarge shi da ɓangaren Nera Tireleyan 1, daga kuɗaɗen da ya ƙwato daga hannun ɓaraye.
Daga nan an naɗa Magu ya gaje shi.
Magu: Daga Nuwamba 2015 Zuwa 2020:
Magu ya shafe shekaru biyar Majalisar Dattawa ba ta tantance shi ba.
Ya samu rashin jituwa sosai da tsohon Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Malami, har aka cire shi, tare da kama shi.
Abba Mohammed: Daga 2020 Zuwa 2021:
Abdulrashid Bawa: Daga 2020 Zuwa 2023:
Abdulkarim Chukkol: 2023 Zuwa Yanshe?
Discussion about this post