Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa ya yi barazana da furucin ‘Emlokan a lokacin zaɓen fidda-gwani don kawai ya ci zaɓe.
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana haka a Njebu-Ode, jihar Ogun.
Ya ce dama shi ya na da yaƙinin cewa zai lashe zaɓen 2023, duk kuwa da halin da Najeriya ta shiga bayan sauya launin kuɗi.
Shugaban ya ce ya yi maganar ce ganin yadda a lokacin aka ƙaƙaba rashin kuɗaɗe a ƙasar nan, ga kuma zaɓe ya gabato.
“An ƙwace mana kuɗaɗe, kuma tsarin babu wani alfanu ga baya ga wahala.”
A wancan lokacin an kirkiro sauye sauye da gangar don a kayar da mu a hana mu yin nasara, amma kuma ko a lokacin na ji a jikina nasara na tare da mu.
An canja kudi da gangar, aka kwace mana kudaden mu da karfin tsiya, aka saka talakawa cikin halin kakanikayi don kada mu yi nasara, duk da haka wannan makirci da tsugudidi duk ba su yi tasiri ba, na sara ta zo mana cikin sauki.
Tinubu ya godewa Alake na EgbaLand da sauran sarakunan yankin bisa goyon baya da su ka bashi.
“Da ma dai nan na zo gaban ka na ikirarin Emilokan, na ce maka zan tafi yakin neman zabe, to gashi kamar yadda na yi alkawari na dawo in nuna maka ganimar nasarar yaki har gida, Allah ya bamu nasara a karshe.
Discussion about this post