Kungiyoyin Ma’aikatan lantarki da na Ƴan jaridar da na Kwadago gabaɗaya za su tsunduma yajin aikin gama gari a fadin kasar nan daga ranar Laraba mai zuwa.
Kungiyoyin gaba ɗayan su za su fara yajin aikin ne dalilin cire tallafin mai da gwamnatin Bola Tinubu ta yi.
Idan ba a manta ba, gwamnatin Tinubu ta sanar da cire tallafin mai daga ranar 29 ga Mayu.
Tinubu ya ce dama kuma babu kudin biyan tallafin a cikin kasafin kudin 2023, wanda ya bashi daman dakatar da biyan kudin tallafin.
Shugaba Tinubu ya kara da cewa ” Ya zama dole a cire tallafin mai da ake biya idan har ana so a samu ci gaba mai dorewa a kasar nan. Wasu ne ake biya waɗannan kudade bagas, yayin da mutanen kasa na fama cikin tsananin talauci.
Sai dai kuma tun bayan sanar da dakatar da cigaba da biyan kuɗin tallafin mai din farashin mai ya yi tsahin gwauron zabi.
Kamfanin mai na kasa da kanta ta sanar da karin kudin mai wanda ya tashi daga N190 zuwa Naira N540 duk lita daya.
Wannan karin ya sa talakawa sun faɗa cikin mawuyacin hali a kasar nan.
Harkar sufuri ya tashi sannan kayan abinci ya lola sama sosai.
Dalilin haka ya da kungiyoyi da ban daban suka fito suka sanar da fara yajin aiki daga ranar Laraba mai zuwa.
Wannan yajin aiki zai kara saka mutane musamman talakawa cikin tsanani da kunci wanda cire tallafin bai saka su ba.
Discussion about this post