Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq a ranar Litinin ya gana da jiga-jigan kungiyoyin kwadago a jihar, inda ya yi kira gare su da cewa cire tallafin man fetur da aka yi an yi shi ne domin dakile barnata kudin gwamnati da ake yi da kuma don bunkasa tattalin arzikin kasa.
Hakan ya biyo bayan rage ranakun aiki da gwamnati ta yi domin rage radadin cire tallafin mai da mutane ke fama da shi.
Yanzu haka ma’aikatan gwamnati za su yi aiki na tsawon kwanaki uku ne a jihar Kwara, sabanin kwanaki biyar da ake yi yanzu.Gwamnati zata fitar da jadawalin yadda za a rika aikin karba-karba musamman ga ma’aikatan asibitoci da malamai.
” Cire tallafin mai da gwamnati ta yi, tsananin takura ne ka mutane amma kuma babu yadda za a yi idan ba hakan aka yi ba domin ita ce hanya daya tilo da za a bi wajen dakile harkallar satar kudin kasa da wasu kalilan suke yi domin aljihun su da sunan tallafin mai.
” Yanzu da bashi ma a cikin kasafin kudin kasa, duk da an cire tallafin ma, abin da gwamnati ta ke so ta yi shine a zauna da kungiyoyin kwadago a duba yadda kudaden zai amfani mutanen Najeriya baki daya ba wasu tsiraru da ke lamusge shiba.
Duka kungiyoyin Kwadago na jihar ne suka halarci taron.
Discussion about this post