Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke duk wata hada-hadar musayar naira da kuɗaɗen waje da bankuna ke yi, ta hanyar karɓo dala da fam daga CBN ana canjarwa.
Wannan shiri ya na nufin gwamnati ta daina bambanta farashin dala daga bankuna da farashin ‘yan canji.
Haka nan kuma CBN ya soke shirin RT200, shirin da Emefiele ya shigo da shi bisa tunanin ƙara samun shigowar kuɗaɗen waje, musamman dala daga ƙasashe zuwa cikin Najeriya.
Wannan tsari dai zai fara aiki ne daga ranar 30 Ga Yuni.
Gwamnatin Najeriya ta ce ya yi hakan ne domin a ƙara samun masu zuba jari daga waje, waɗanda za su riƙa shigo da dala a cikin ƙasa, domin tattalin arziki ya bunƙasa.
Daga ranar 30 Ga Yuni za a daina sayar wa ‘yan kasuwar tsaye dala su na biya da Naira, sannan su kuma su sayar da Dalar ga masu buƙata.
Sanarwar da Daraktan Hada-hadar Kasuwanci na CBN ta fitar a ranar Laraba, Angela Sere-Ejembi ta ce CBN ya soke bambanta tsarin musayar kuɗaɗen waje, ya mayar da tsarin na bai-ɗaya.
“Duk wata harkar hada-hadar kuɗaɗen waje za ta koma ana yin ta a ƙarƙashin tsarin I&E, ta hanyar masu zuba jari daga waje da kuma masu fitar da kaya daga cikin gida Najeriya zuwa ƙasashen waje.
Sai dai kuma sanarwar ta ce ba banki zai ci gaba da bayar da dala ga masu fita waje neman lafiyar su, masu biyan kuɗin makarantar ɗaliban da ke karatu makarantun waje.
Kuma za a ci gaba da biyan jami’an gwamnatin da aka tura aiki wane ko yin kwas.
CBN ya bar naira ta ceci kan ta a kasuwa, lamarin da ya ke ganin hakan zai ƙara mata ƙarfi da daraja.
Sai dai kuma tuni hankulan ‘yan canji ya tashi, su na tunanin lokacin mutuwar kasuwar su ya yi kenan.
Cire Hannu Gwamnati A Sha’anin Dala:
Hakan ya na nufin bankuna su yi cinikin dala yadda su ka ga dama. Kuma hakan na nufin yawan shigowar dala cikin ƙasa da yawan buƙatar ta, shi ne zai iya ƙayyade yadda farashin ta zai iya kasancewa a kasuwa.
Sai dai kuma masu nazari da masu canji sun nuna cewa lamarin ka iya janyo farashin dala ya yi tashin-gwauron-zabo.
Hakan kuwa ka iya kasancewa ne sai fa idan yawan buƙatar dala ya zarce yawan adadin wadda ake iya samu a ƙasar nan.
Wasu na ganin cewa kafin a warware idan ma har an kama hanyar warwarewar, to za a iya fuskantar matsalar hauhawar farashin kayan masarufi, musamman waɗanda ake shigowa da su.
Babban abin da ya fi tayar wa ‘yan canji hankali shi ne tsarin ka iya ruguje tubulan kasuwancin su.
Discussion about this post