Cibiyar Nazarin Gine-gine ta Najeriya NIA ta yaba rushe-rushen da gwamnatin jihar Kano ke yi a jihar.
Cibiyar ta fadi haka ne a Wata sanarwa da sakataren yada labarai na gwamnan jihar Abba Yusuf, Malam Bature Dawakin-Tofa ya fitar ranar Laraba a garin Kano.
Shugaban kungiyar Enyi Ebo ya yi kira ga gwamnati da ta yi amfani da sabuwar tsarin gine-gine da hukumar ta fitar domin hana mutane yin gini yadda suka so batare da an bi doka ba.
Ya kuma yaba wa gwamnan Abba Yusuf bisa wannan aiki na rusa gine-ginen da ba ayi su bisa ka’ida ba sannan da kuma wadanda suka saba wa dokar cibiyar.
Bayan haka gwamnan wanda Shugaban ma’aikatan fadan gwamnati Shehu Sagagi ya wakilta ya mika godiyarsa ga kungiyar yana mai cewa lallai gwamnati za ta yi duk abinda ya dace domin gyara jihar Kano da kuma maida shi abar alfahari da a tsakanin jihohin kasar nan.
Shehu Sagagi ya ce zuwa yanzu gwamnati na kokarin samar da abinci wa makarantun sakandare na kwana mallakin gwamnati, kwashe Bola a fadin jihar, saka wutan lantarki a titi da bude wuraren horas da matasa da mata sana’o’in hannu.
Idan ba a manta ba tun bayan rantsar da gwamna Abba Yusuf ya kaddamar da aikin rushe rushen gineginen da ba ayi su bisa ka’ida ba a duk fadin jihar.
Discussion about this post