Jami’in Hukumar Alhazai Alhussain Maiwada ya bayyana cewa Alhazan jihar a Maka sun gama shiri tsaf domin halartar Hawan Arafat, wanda za a yi gobe Talata.
Maiwada ya ce, komai na tafiya yadda ya kamata l, sannan mahajjata duk sun ɗunguma zuwa Minna domin shirin yin wannan babban aiki na Hawan Arafat.
Discussion about this post