Direbobin motocin haya a jihar Kaduna sun koka da yadda ba sa samun fasinjoji saboda karin farashin kudin mai da mota da aka samu.
A tashoshin mota a Kaduna da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta ziyarta ta ga cewa babu fasinjoji kamar yadda aka saba samu a baya musamman a lokacin shagulgula irin haka.
Wasu direbobin sun ce yayin da ake shirin Babban Sallah kamata ya yi tashoshin mota suna cika da mutane matafiya sai dai bana ba hakan ke faruwa ba.
Sarkin Musulmi Saad Abubakar ya sanar da ranar 28 ga Yuni ranar Babban Sallah.
Wani direba dake jigilar fasinja daga Kaduna – Abuja a ‘Command junction’ David Turaki ya ce kudin mota ya tashi daga naira 2,500 zuwa 4,000 tun bayan da aka cire tallafin man fetur.
A tashar Sabo Wani direba Musa Adireba ya ce farashin kudin mota daga Kaduna zuwa Kafanchan ya tashi daga 3,000 zuwa 4,000 sannan daga Kaduna zuwa Jos ya tashi daga 5,000 zuwa 6,000.
“ Wasu lokuta haka nake tafiya Koda motan bai cika ba, sai in bi hanya ina rarumen fasinjoji.
A tashar Kawo Jamilu Idris ya ce daga Kaduna zuwa Zariya suna daukar fasinjoji kan 1,500 daga 700 sannan daga Kaduna zuwa Kano ya koma 5,500 daga 4,000.
Shima Abubakar Jibril dake tashar Kawo ya ce daga Kaduna zuwa Sokoto ya tashi zuwa 8,000 daga 4,500. Sannan Kaduna zuwa Katsina ya koma 9,000 daga 4,500.
Wani ma’aikacin gwamnati kuma fasinja a tashar Kawo Addo Bisallah ya ce kullum yake shiga mota daga Kaduna zuwa Zariya amma yanzu baya iya yin haka sai dai ya jira karshen mako sannan ya tafi Zariya.
Wani jami’in kungiyar NURTW Nasidi Garba ya ce kungiyar ta dauki wasu matakai da za su taimaka wajen karkato da hankalin gwamnati domin kawar da wadannan matsaloli.
Discussion about this post