Kamar yadda mu ka sha fada a baya, tabbas kowa yaji a jikin sa, mussamman mutanen da masifar ambaliyar ruwan ta shafa kai tsaye a wannan jaha tamu.
Ko a baya mun sha musanyar yawu dama rashin fahimta, musamman da mutanen da suke ga su kadai ne suke kusa da masu iko.
A baya, tabbas an samu tasgaro ko kuma halin ko in kula daga bangaren masu mulki, wajen tunkarar zuwan ambaliyar, dama dagewarsu wajen yakar abun ka’in da na’in.
Kamar yadda kowa yasan yanayin da al’ummar mu ke shiga duk lokacin da wannan masifa ta ambaliyar ruwa tazo a duk lokacin Allah ya jarrabce mu da masifar.
Kai ban da asarar gonakai, muhallai da dukiyoyi, ita ma kanta Gwamnatin na asara marar adadai.
Amma a bana, ga dukkan alamu, larabar mu za tayi kyawu, ganin yadda suka chanja tsarin tunkarar wannan matsalar.
Dama an ce rigafi ya fi magani, ganin yadda Gwamnatin jahar Jigawa karkashin jagoran cin Malm Umar Namadi a kankanin lokaci ta ke aiki ka’in da na’in wajen toshewa da gyaran hanyoyin da ruwa ke haddasa ambaliya.
Imani da kwarin gwiwar da jama’a suka samu, cewar a yau, wannan Gwamnatin hankalin ta a tashe yake wajen ganin yiwa al’ummar mu rigakafin zuwan ambaliyar.
Babban kwarin gwiwa shine ganin yadda Maigirma Gwamna, ya kasa zama yana kewayen wuraren da a ke aiyukan jinga da gyara hanyoyin da ruwa ke bi.
Tabbas irin wannan yunkuri sabo ne a idanuwan mutanen Jigawa, wanan na nuni da cewa, wannan Gwamnatin a kwai ruhin talaka a tare da ita, kuma yanayin da mutane ke shiga sanadiyyar wannan masifa ta same su.
Amma muma fa dole sai mun bada tamu gudunmawar, don mu gudu tare, mu tsira tare.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post