AIKI SAI MAI SHI: Yari ya raba wa talakawa 500 ragunan Layya a Zamfara
Tsohon gwamnan Zamfara, AbdulAziz Yari ya raba wa talakawan jihar 500 ragunan layya.
Shugaban kwamitin rabon kayayyakin, Sha’aya Sarkin-Fawa ne ya bayyana haka a lokacin da yakeraba ragunan a karamar Hukumar Talatan Mafara.
” Wannan abu ne wanda shugaban mu Yari ya saba yai domin taimakawa Talakawa suma su samu yin Layya a wannan lokaci.
“Wannan na makwabtansa ne, gidaje marasa galihu, ‘yan gudun hijira (IDP) da marayu da ke cikin garin Talata-Mafara kawai. Wannan baya ga raguna 1,000 da shanu 400 da ya bayar a baya ga shugabannin jam’iyyar APC da kuma wasu ‘Yan jam’iyyar ne a baya.
A karshe Sarkin Fawa ya yi kira ga mutanen da suka amfana da wannan kyaututtuka da su ci gaba da yi wa kasa addu’a da kuma fatan Allah ya kara mana zaman lafiya da ci gaba.
Discussion about this post