Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta ware kudade domin biyan jarabawar kammala makarantar sakandare na NECO wa dalibai 55,000 dake karatun sakandare a makarantun gwamnati a jihar.
Gwamnan jihar Abba Yusuf ya sanar da haka a lokacin da yake bayani kan ayyukkan da gwamnatinsa ta yi bayan kwanaki 20 da rantsar da ita.
Yusuf ya yi kira ga daliban jihar wadanda za su rubuta jarabawar su zage damtse sannan su yi karatu karatu domin samun nasara a jarabawar cewa yin haka zai kara karfafa gwiwar gwamnatin wajen ci gaba da bunkasa ilimi a jihar.
“ Gwamnatin mu, gwamnatin jama’a ce sannan gwamnati mai kishin talaka da kuma wanzar da ilimi ce, wannan shine dalilin da ya sa muka kamfaci kudi daga asusun gwamnati domin biya wa ‘yayan talakawa kudin jarabawar kammala sakandare.
Gwamna Abba ya ce gwamnati za ta ci gaba da bunkasa ilimi a jihar sannan ta kara fadada hakokin kasuwanci da ci gaban al’aumma a fadin jihar.
Discussion about this post